1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ministocin harakokin wajen EU a Brussels

July 17, 2006
https://p.dw.com/p/BuqF

A cen ma cibiyar ƙungiyar gamaya turai, da ke Birnin Brussels na ƙasar Belgium . ministocin harakokin wajen na ƙasashen EU, na ci gaba, da tanttanawa, akan rikicin Isra´ila da Hezbollah.

Ranar jiya lahadi, sakataran harakokin wajen EU, Havier Solana ya kai ziyara akasar Labanon domin gani da ido halin da ake ciki.

Kamin Solana ya bayyana rahoton ziyara ta sa, ministocin ƙungiyar harakokin wajen ƙungiyar gamaya turai, na shirin hiddo sanarwar haɗin gwiwa, a kan matakan yafa ruwa, ga wutar rikicin Isra´ila da Labanon.

Ministan harakokin wajen Spain, Miguel Angel Maratinos, bugu da ƙari, tsofan wakilin EU, a yankin gabas ta tsakiya, ya yi kira da babbar murya, ga ƙungiyar gamayya turai, ta ɗauki mattakai ƙwaƙƙwara, wanda za su taimaka, a kawo ƙarshen yaƙin, a maimakon sabbatu na fatar baki.

Bayan halin da ake ciki a gabas ta tsakiya, ministocin harakokin wajen EU, za su tantana rikicin yanki Darfur na ƙasar Sudan, tare da halartar sakatare Jannar na Majalisar Ɗinkin Dunia Koffi Annan.