1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU na nazarin kakabawa Rarsha takunkumi

Zainab Mohammed Abubakar
October 12, 2020

Faransa da Jamus sun gabatar da kudurin san ya takunkumin bayan binciken da ya tabbatar da cewar, an yi amfani da nau'in gubar Novichok a kan dan adawar.

https://p.dw.com/p/3jmLh
Coronavirus I Außenminister Heiko Maas
Hoto: Kay Nietfeld/AFP/Getty Images

Ministocin harkokin wajen tarayyar Turai na shirin gudanar da taro a wannan Litinin, domin samar da mafita kan matsalolin ketare masu tarin yawa da suka hadar da yiwuwar kakaba wa Rasha takunkumi kan zarginta da hannu a sanya wa madugun adawar kasar Alexei Navalny guba.

Kasashen Jamus da Faransa da suka gabatar da wannan bukatar, na da yakinin cewar, amfani da gubar zai iya nasara ne kawai da sa hannun mahukuntan kasar ta Rasha.

Sanarwar hadin gwiwa tsakanin ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas da takwaransa na Faransa Jean-Yves Le Drian, na nuni da cewar takunkumin zai shafi jami'ai da wasu hukumomin gwamnati.