1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a mayar da Siriya cikin Kungiyar Larabawa

Mahmud Yaya Azare RGB
April 14, 2023

Bayan kwashe shekaru 12 suna mayar da ita saniyar ware, Saudiya ta shirya wani gagarumin taron kasashen Larabawa don mayar da kasar Siriya cikin dangi.

https://p.dw.com/p/4Q7RZ
Shugaba Assad da Sheikh Mohammed bin Zayed
Shugaba Assad da Sheikh Mohammed bin ZayedHoto: Syrian Presidency/apaimages/IMAGO

Bayan kwashe shekaru 12 suna mayar da ita saniyar ware, daga karshe, Saudiya ta shirya wani gagarumin taron kasashen Larabawa guda 9 don mayar da kasar ta Siriya cikin dangi, lamarin da ke ci gaba da jawo martanoni mabanbanta.

Kamar yadda a shekarar 2012, kasar ta Saudiya ta jagoranci gangamin mayar da kasar ta Siriya saniyar ware ta hanyar katse hulda da ita da korarta daga kungiyar kasashen Larabawa, gami da bai wa masu ta da kayar baya ma gwamnatin Shugaba Bashar-Al-Asad makamai don su tunbuke shi daga mulki da karfin tuwo, a wannan karon ma, kasar ta Saudiya ce ke jagorantar gangamin dawo da kasar ta Siriya cikin dangi da ma fatan ganin ta halarci taron kasashen Larabawan da Saudiyan za ta dauki bakwancinsa a wata mai zuwa.

Zauren taron Kungiyar Kasashen Larabawa
Zauren taron Kungiyar Kasashen LarabawaHoto: AFP/Getty Images

 Taron da ke gudana a birnin Jeddah tun daga wannan Jumma'a, da ya kunshi wakilan kasashen Larabawa tara na zuwa ne, bayan ziyarar da Ministan Harkokin Wajen Siriya ya kai, wadda ita ce irinta ta farko tun bayan barkewar yakin basasa a kasarsa a shekarar 2011, kamar yadda yake zuwa bayan sake bude ofishin jakadancin Iran a birnin Riyadh na Saudiya, biyo bayan dinke baraka da sasantasu da kasar Chaina ta yi nasarar yi a watan da ya gabata.

Rikicin kasar Siriya ya raba miliyoyi da gidajensu
Rikicin kasar Siriya ya raba miliyoyi da gidajensuHoto: UNICEF/UNI326167/Albam

Duk da cewa, galibin kasashen Larabawan da ke halartar wannan taro, suna goyan bayan mayar da kasar ta Siriya cikin dangi, sai dai wasunsu na dagewa kan cewa, sai idan gwamnatin ta Siriya ta sasanta da 'yan tawaye, kana ta biya diyyar miliyoyin wadanda aka kasea da ma kafa rundunar Larabawa ta tabbatar da zaman lafiya a kasar ta Siriya, kafin su lamunta a mayar da ita cikin dangi, ba a Kungiyar Larabawa kadai ba, har ma da sauran kasashen duniyar da ke sanya mata takunkumi kan kisan kiyashin da ake zargin ta yi wa 'yan kasarta, wanda ya kai ga jerantashi cikin manyan laifufukan yakin da har kotun duniya ta fitar da sammacin kama shugaban na Siriya da mukarrabansa don hukuntasu.

 Amurka da Tarayyar Turai gami da kungiyoyin kare Hakkin bil Adama na mummunar adawa da mai da Shugaba Assad cikin dangi, sai dai masharhanta na cewa, wannan ba shi ne karon farko da suke lashe amansu, su dawo da yin hulda da shuwagabanin kama karya don kare muradunsu ba. Tuni gamayyar kungiyoyin 'yan tawayen Siriya ta siffanta wannan taron da taron yankan baya ga al'umar Siriya.