1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Putin zai gana da Assad a birnin Mosko

Ramatu Garba Baba
March 15, 2023

Shugaba Bashar al-Assad na ziyarar Rasha a gabanin cika shekaru 12 da barkewar yakin basasan da ya daidaita kasar Siriya tare da tilasta wa miliyoyi zama 'yan gudun hijira.

https://p.dw.com/p/4Ogv2
Shugaba Bashar al-Assad a lokacin da ya isa birnin Mosko
Shugaba Bashar al-Assad a lokacin da ya isa birnin MoskoHoto: SANA/AP/picture alliance

A wannan Laraba Shugaba Vladimir Putin na Rasha zai gana da takwaransa na Siriya Bashar al-Assad a birnin Mosko a yayin wata ziyara mai tattare da tarihi da shugaban na Siriya ke kai wa Rasha da ke shan suka daga manyan kasashen duniya a sakamakon matakinta na mamayar Ukraine. 

A wata sanarwa da fadar Kremlin ta fitar a ranar Talatar da ta gabatam ta ce, shugabanin za su tattauna batutuwan da suka shafi ci gaba da bunkasa harkokin kasuwanci da tattalin arziki da kuma ayyukan jin kai ga kasar da ta gamu da iftala'in girgizar kasa da kuma fatan daidaita yanayin rikicin da ake fama a cikin Siriya da kewaye. Ziyarar na zuwa ne a gabanin cika shekaru goma sha biyu cif da soma yakin basasa a Siriya wace Rashan ke goyon bayanta.