1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya: Kasashen Larabawa sun gana da al-Assad

February 26, 2023

Wata tawaga ta 'yan majalisun dokokin kasashen Larabawa sun gana da shugaban Bashar al-Assad na Siriya a birnin Damascus a wani mataki na farfado da dangantaka da Siriya.

https://p.dw.com/p/4O0EE
Syrien Damaskus | Treffen Ayman Safadi, Außenminister Jordanien & Bashar al-Assad
Hoto: Syrian Presidency via REUTERS

Tawagar dai ta hada da wakilan kasashen Jordan da Falasdini da Libiya da Masar da Hadaddiyar Daular Larabawa da Oman da kuma Lebanon. A cewar dan majalisar dokokin Iraqi Mohammed Halbousi ya ce, tsakaninsu da kasar Siriya tamkar dan juma ne da dan jumai domin haka suke fatan alaka ta sake karfafa a tsakaninsu. Dangantaka dai ta fara inganta tsakanin kasar da sauran takwarorinta ne tun bayan da ta fuskanci mummunar girgizar kasar a farkon wannan watan na Fabarairu wanda ya halaka mutane kimanin dubu 6 a Siriyar.

Kasar Siriya dai ta kasance mujiya a cikin tsintsaye a tsakanin kasashen Larabawa tun bayan da shugaba al-Assad ya murkushe masu zanga-zanagar adawa da gwamnatinsa a shekarar 2011. A shekarar ce kuma kungiyar kasashen Larabawa ta dakatar da kasar Siriya daga zama mamba a cikinta, yayin da kasashe da dama suka janye jakadunsu daga birnin Damascus.