1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya: Likita mai azabtar da mutane

Matthias von Hein AH/LMJ
February 3, 2022

An fara shari'ar wani likita dan kasar Siriya a birnin Frankfurt na Jamus, bisa zarginsa da azabatar da masu adawa da gwamnatin Bashar al-Assad.

https://p.dw.com/p/46Swi
Jamus Frankfurt shari'ar likitan da ya azabtar da mutane a Siriya
Likitan da ya azabtar da mutane a Siriya a gaban kuliya, tare da lauyansaHoto: Boris Roessler/dpa/picture alliance

Likitan mai suna Alaa Musa dan shekaru 35 ya isa Jamus tun a shekara ta 2015, a matsayin ma'aikaci ba dan gudun hijira ba. Tun lokacin da ya shiga Jamus din yake yin aiki a cikin asibitoci dabam-dabam har zuwa lokacin da aka kama shi a cikin watan Yuni na shekara ta 2020, inda a yanzu haka zai fuskanci hukunci a Jamus din. A kasarsa Siriya  dai, ana girmama likitoci kan irin gundunmawar da suke bayarwa. Sai dai wasu likitocin ana amfanin da su wajen azabtar da mutane musammun masu adawa da  gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad.

Karin Bayani:Sharhi kan shekaru 20 na shugabancin Assad

Ana dai tuhumar Alaa Musa da laifuka 18 na azabatarwa da kisa ta hanyar yin alura ga wani fursuna yayin da yake aiki a wani asibitin sojoji a garin Homs a shekara ta 2011, inda nan ne tungar 'yan adawa. Daga bayanan da aka tattara na lokacin da yake Siriya, likitan ya rika musgunawa dukkan wadanda aka ba shi umurni a kansu. A wani bincike da Farfeser Houssan al Nahhas da shi ma ya kasance likita wanda kuma ya fuskancin azabatarwa a Siriya, ya ce likitocin na da dabaru na azabatarwa wanda ko mutum ya mutu ba a gane cewar an azabatar da shi.

Siriya I Sojojin Amirka sun kashe shugaban kungiyar IS
Dubban mutane ne dai, yakin kasar Siriyan ya tarwatsaHoto: Aaref Watad/AFP

Ba wai a Siriya kawai ne ake samun wannan al'amari na azbatarwar likitoci ba. A wani rahoto da ta fitar, kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty Intrnational ta bayyana kasashe 140 inda likitocin ke azabtarwa. A Jamus ma lokacin gwamnatin 'yan Nazi, likitocin sun taimaka wajen aikata kisa ta hanyar azabtarwa. Daya daga cikinsu shi ne likita Josef Mengele da ake wa lakabi da mala'ikan mutuwa, wanda ya rika fesawa fursuna iskar gas mai guba.

Karin Bayani: Yaki ya sake haddasa mutuwar fararan hula a idlib

Kusan rabin karni kenan dai, kungiyar likitoci ta duniya take yin adawa da azbatarwa ta hanyar amfani da likitoci wanda ta yi haramci a kai a taron birnin Tokyo da aka yi a 1995. Sai dai abin takaici har kawo yanzu a cikin kasashen da ake bin tsarin dimukuradiyya, ana yin amfanin da azabatarwar litkitocin. Misali a Amirka, akan yi amfani da azabtarwar domin yaki da ta'addanci. Gidajen Fursunoni kamar  Gwatanamo da Abu Ghraib, duk ba su fita daga cikin wannan tsarin ba.