Taron kolin AU ya ja hankalin jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 12.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Taron kolin AU ya ja hankalin jaridun Jamus

Bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar kasuwanci maras shinge a tsakanin kasashen Afirka yanzu abin jira shi ne ko kasashen za su cika alkawuran da suka dauka na sakar wa harkokin kasuwancin mara?

A sharhin da ta buga dangane da taron kungiyar Tarayyar Afirka AU jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta fara ne da cewa wani yankin kasuwanci maras shinge zai fara aiki a Afirka, bayan da kungiyar Tarayyar Afirka AU a taronta na birnin Yamai ta amince da yarjejeniyar kasuwanci maras shinge tsakanin kasashen Afirka. Bisa ka'idojin yarjejeniyar, nan da wasu shekaru masu zuwa za a samu yankin kasuwanci maras tarnaki mafi girma a duniya a tsakanin kasashen na Afirka. Jaridar ta ce yanzu haka dai huldar kasuwanci tsakanin kasashen na Afirka ba ta taka kara ta karya ba saboda yawan haraji da yawan dogon turanci da rashin kyawawan hanyoyin sufuri wanda ke kawo cikas a harkokin kasuwanci da na tattalin arziki a tsakanin kasashen. Jaridar ta kara da cewa abin jira a gani shi ne ko kasashen na Afirka za su cika alkawuran da suka dauka na sakar wa harkokin kasuwancin mara ko kuma wasu daidaikun kasashe za su ci gaba da sanya tarnaki.

Niger Treffen der afrikanischen Union in Niamey - Muhammadu Buhari (Getty Images/AFP/I. Sanogo)

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Jaridar Neue Zürcher Zeitung cewa ta yi yayin da ake maraba da wannan yarjejeniya da ke da burin samar da yankin kasuwanci maras shinge mafi girma a duniya, abin tambaya shi ne saye da sayarwa tsakanin kasashe na da ma'ana ne kawai idan kasa na da wata haja da za ta iya sayar wa 'yar uwanta da ba ta da irin wannan haja ko kuma tana da tsada a kasar. Kasancewa a Afirka babu isassun masana'antu masu sarrafa danyun kayan da akasari kasashen nahiyar ke samarwa, dole Afirka za ta ci gaba da dogaro da manyan kasashe masu ci-gaban masana'antu. Kasashen kuma na da karancin wuraren adana kayan amfanin gonar da yawancinsu ke samarwa.

Hukuncin ICC kan Ntaganda

Niederlande Internationaler Gerichtshof Prozess Bosco Ntaganda Den Haag (Reuters/M. Kooren)

Ntaganda madugun 'yan tawaye Kwango

An yanke wa madugun 'yan tawayen Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, Bosco Ntaganda hukuncin a kotun kasa da kasa da ke birnin The Hague, wannan shi ne taken labarin da jaridar Süddeutsche Zeitung ta buga a tsokacin da ta yi na zaman shari'ar da aka yi wa madugun 'yan tawayen na Kwango da ake wa lakabi "Terminator". Kotun ta sami Ntaganda mai shekaru 45, da laifukan yaki 13 da kuma wasu laifuka biyar da suka hada da kisan kai da fyade tare da cin zarafin al'umma a lokacin rikicin kasar Kwango tsakanin shekarun 2002-2003 lokacin da yake rike da mukamin mataimakin shugaban sojojin sa kai. Sai dai Ntaganda ya musanta tuhumar.

Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung ta leka arewacin Najeriya ne musamman a Kaduna inda ta ruwaito wani kokari da ake yi na kawo karshen kin bayyana matsalar fyade da ake wa kananan yara. Jaridar ta ce a arewacin Najeriya ba kasafai ake fitowa fili a yi magana game da cin zarafin ta hanyar lalata da yara ba, sau da yawa ana tilasta wa wadanda abin ya shafa su kame bakinsu su yi shiru, wai don kare mutuncin gida. Yanzu an fara wata yekuwa ta intanet mai taken #ArewaMeToo don kawo canji a cikin al'ummar arewacin Najeriya mai ra'ayin mazan jiya.