Taron kan Girka ya tashi da babu | Labarai | DW | 19.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron kan Girka ya tashi da babu

Shugabar Aususun bada lamuni na duniya wato IMF tace ba za ta sabu ba Girka ta jinkirta biyan bashin dake kanta a karshen watannan.

Christine Lagarde ta na magana ne bayan da ministocin kudin kasashen da ke amfani da Euro suka kammala wani taronsu a Luxembourg jiya Alhamis ba tare da cimma matsaya ba. Sai dai an ruwaitio shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel na cewa, Jamus na son Girka ta ci-gaba da zama cikin kasashe masu amfani da Euro, don haka akwai damar sasantawa da masu bada bashi, muddin dai mahukuntan Girka na da niyyar hakan. Ministan kudin kasar ta Giraka shi kuwa zargin masu bin kasar bashi ya yi da cewa, su na damuwa ne kawai da al'amuran da suka shafe su, basa yin la'akari da ita Girka ko kadan cikin tattaunawar.