1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

G20: Aniyar kawo karshen annobar corona

Mouhamadou Awal Balarabe MNA
November 23, 2020

Taron koli ta yanar gizo na shugabannin kungiyar G20 da Saudiyya ta dauki bakonci, ya kuduri aniyar kawo karshen annobar corona, sannan batun alkinta muhalli shi ma ya kasance a kan gaba na matsalolin da aka tattauna.

https://p.dw.com/p/3lieT
G20 Gipfel Saudi Arabien | Gruppenfoto digital
Hoto: Präsidentschaft G20 Saudi Arabien Pressestelle

Wannan shi ne karon farko da wata kasa ta Larabawa ke karbar bakoncin taron koli na kasashe 20 da suka fi karfin masana'antu na duniya - ko da shi ke an yi amfani da kafofin sadarwa na zamani wajen gudanar da shi. Tabbas annobar corona ce ta mamaye zaman, inda Kungiyar G20 ta kuduri aniyar farfado da tattalin arzikin kasashen da suka fi karfin masana'antu bayan lafawar annobar corona da ake fama da ita. Hakazalika shugabannin sun bai wa matakan yaki da sauyin yanayi fifiko. Ko da Narendra Modi, firaministan Indiya sai da ya ce dole ne a hada karfi da karfe wajen yakar sauyin yanayi idan ana son samun biyan bukata, lamarin da  Xi Jinping, shugaban kasar Sin ya yi na'am da shi.

"Ya Kamata G20 ta ci gaba da daukar matakan magance canjin yanayi. Muna bukatar bin jadawalin da Majalisar Dinkin Duniya ta shimfida tare da matsa kaimi wajen aiwatar da yarjejeniyar mai inganci ta Paris kan canjin yanayi."

A takaice dai yawancin shugabannin sun karkata kan bukatar kare duniyar - amma kuma a salon da ya saba, Shugaban Amirka Donald Trump ya kare matakinsa na ficewa daga yarjejeniyar birnin Paris. Hujjojin zuwa taron G20

"Ba a tsara yarjejeniyar ta Paris don kare muhalli ba, an tsara ta ne don kashe tattalin arzikin Amirka. Na ki mika miliyoyin ayyukan Amirka tare da tura tiriliyoyin daloli ga mafi munin matakin gurbata muhalli da masu cin zarafin muhalli, kuma abin da zai faru kenan."

Virtueller G20-Gipfel unter Vorsitz Saudi-Arabiens I Angela Merkel
Hoto: Guido Bergmann/Bundesregierung/dpa/picture alliance

Sai dai a nata bangare shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da ta cika shekaru 15 a kan kujerar mulki a ranar Lahadi, ta jaddada bukatar taimaka wa kasashe matalauta don magance mummunan tasirin da annobar coronavirus ta yi a kan tattalin arzikinsu.

"A karo na farko a cikin lokaci mai tsawo mun ga karuwar talauci a duniya. Ya kamata mu yi tsayuwar daka kan wannan matsalar. A taronmu na yau mun jaddada muhimmancin saka hannun jari na 'yan kasuwa, musamman a nahiyar Afirka."

Mai masaukin baki, Sarki Salman na Saudiyya ne ya rufe taron da sako mai dadi, inda ya ce za su fuskanci alkibla guda wajen kawo karshen annobar Covid-19.

"Mun tabbatar da kudurinmu na yin aiki tare don fuskantar kalubalen annobar Covid-19, don kiyaye rayuka da hanyoyin samun abinci da kuma kare wadanda suka fi rauni."

Dukkanin membobin G20 sun raja'a kan allurar rigakafin coronavirus da ake habakawa kuma shugabannin kasashen da suka fi ci-gaba sun yi akwarin samar wa kasashe matalauta cikin farashi mai rahusa. Babu wani adadin kudi na zahiri da aka kayyade, amma shugabar gwamnati Angela Merkel ta yi kamfen kan Euro biliyan biyar da aka riga aka tara, wanda za a ninka shi domin samar da kudade na kusan allurai biliyan biyu.