1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taro domin nazarin aikin kotun ICC

November 24, 2016

Najeriya ta jaddada goyon baya ga kotun duniya mai hukunta manyan laifukan yaki ta duniya ICC, yayin da wasu kasashen Afirka ke fita daga kotun.

https://p.dw.com/p/2TAXN
Fatou Bensouda Chefanklägerin am ICC
Hoto: ICC

Kama daga Gambia zuwa Burundi da Afirka ta Kudu dai sannu a hankali kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa da ke birnin Hague na fuskantar karin turjiya dama tawaye daga kasashen da ke mata kallon karen farautar Turawan yamma. A baya dai kasashe da yawa da suka hada da Najeriya sun yi watsi da umarnin kotun na kama shugabanni kamar na Sudan da ta ce tana nema ruwa a jallo.

Den Haag Internationaler Strafgerichtshof Prozess Jean-Pierre Bemba
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Kooren

A cikin wannan mako ne dai kasashen da suka kai ga rattaba hannu a yarjejeniya ta birnin Roma da tai nasara kafa kotun ke wani taro na musamman da nufin nazari ga barazana ta ficewar da hadin kan da kotun ke samu a tsakanin kasashe.

To sai dai kuma da alamu duk da hukunci na kasashen na Afirka da dama a cikin gida Najeriya, har yanzu da sauran tagomashi ga kotun a tsakanin 'yan mulki na kasar. Gwamnatin kasar dai ta ce ba ta da niyyar bin sahun dangi wajen fita daga kotun wadda kasashen na Afirka ke yi wa kallo wata kafa ta tozarta su a ido duniya.

Den Haag Internationaler Strafgerichtshof Prozess Jean-Pierre Bemba
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Kooren

Geoffrey Onyeama shi ne ministan harkokin wajen Najeriya, kuma ya ce har yanzu kotun ta na da sauran kima a idanu na kasar.

To sai dai kuma har yanzu akwai sauran fata na kare muradun nahiyar ta Afirka a bangaren kotun ICC ,daga dukkan alamu dai, a cikin gida wannan fata tsakanin mutane na kara dusashewa sakamakon gaza kai wa ga hukuncin ko'ina a duniya.