Takunkumin Amirka da Tarayyar Turai kan Rasha | Labarai | DW | 17.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Takunkumin Amirka da Tarayyar Turai kan Rasha

Rasha na ci gaba da fuskantar matsin lamba daga kasashen Turai da Amirka, dangane da batun rikicin Ukraine, wanda ake ganin Rasha tana da hannu cikin lamurran.

Kasar Amirka da Tarayyar Turai, sun kara tsaurara matakan takunkumi kan Rasha a yammacin jiya Laraba (16.07.2014), bisa dalilan rawar da take takawa a rikicin Ukraine, inda daga nata bengare kasar Amirka ta dauki matakan da suka shafi fannin tattalin arziki kan kasar ta Rasha.

Sai dai da yake mayar da murtani a yau Alhamis, Shugaban kasar ta Rasha Vladimir Poutine, ya ce iri-irin wannan mataki da Amirka take dauka, na iya gurbatar da dangantakar da ke tsakanin Amirkar da Rasha, kuma hakan zai haifar wa Amirka manya-manyan matsaloli.

Kasar ta Amirka dai ta saka kanfanin sarrafa iskar Gaz din nan na Rosneft na kasar ta Rasha a cikin bangarorin da takunkumin ya shafa, sannan kuma wannan takunkumi zai shafi bankin Gazprom na kasar ta Rasha.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Usman Shehu Usman