Take hakkin bil′ Adama a yankin Diffa | Siyasa | DW | 22.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Take hakkin bil' Adama a yankin Diffa

Wani bi akan kama jama’a bisa zargi ba tare da babban alkalin yankin ya sani ba, kana sau tari wasu jama’ar da aka kama daga yankin na Diffa kan gamu da muzgunawa ko wasu abubuwan da suka zarta haddi.

A Jamhuriyar Nijer Hukumar kare hakkin bani Adam ta kasar mai suna CNDH ce ta wallafa wani rahoton da a ciki ta soki lamirin yadda ake gudanar ayyukan tsaro a yankin Diffa mai fama da matsalar Boko haram,

Abubuwan da suka sabawa tsarin 'yancin bil Adama na kasa da kasa da Nijer ta sakawa hannu, ko baya ga wadannan yanzu hakan inji hukumar da akwai wasu mutane akalla 38 da alkali ya sauraresu ya kuma bayar da belinsu to amma har yanzu jami'an 'yan sanda masu yaki da ta'addanci na rike da su.


Tun daga farko dai tawagar hukumar da ke kare hakkin bani Adaman ta yada zango ne a garin Diffa a ranarkun 17 zuwa 25 ga watan Mayun da ya gabata da zummar gudanar da nata kwakwaran binciken kan yadda ake tafiya dama kiyaye hakkin bani Adama a yankin mai fama da matsalolin ta'addanacin Boko Haram, sai dai hakar hukumar ba ta cimma ruwa sakamakon rashin ingantancen tsaro da kulawa da shuwagabanin yankin ba su bai wa mambobin hukumar ba, saboda hakan hukumar ta takaita ziyarar ne kawai a ganawa da wakilan al'ummomin yankin da na sarakunan gargajiya da malamai da dukkanin masu ruwa da tsaki a kan batun da ke addabar yankin na Diffa.

Sakamakon ganawar dai ya tabbatarwa hukumar cewar game da batun kare hakkin dan Adam a yankin da akwai sauran rina a kaba, hukumar ta ce dokar hana fitar dare da ta hawan babura a yankin sun taimaka wajan rage kaifin matsalar kai hare haren 'yan Boko haram.

Batun noman tattasai da sana'ar kamun kifi da yankin
ya ke bugun gaba da shi da aka dakatar sakamakon dokar tabaci na haifar da tarnaki ga al'ummar jihar inji rahoton hukumar.
Malam Amadou Alichina Koulgeni shi ne babban sakataren Hukumr ta CNDH:
Ya ce "Kamata ya yi gwamnati duk wasu matakan da ta dauka idan ta dauki doka ta dubi yadda za'a dan sawakawa jama'a su samu sauki, lalle dokokin sun taimaka suna da kyau domin an samu kwanciyar hankali a Diffa to amma akwai sauran rina a kaba".


Tuni kungiyoyin fararen hula masu zaman kansu da ke kare hakkin bani Adama suka yaba da jin rahoton na hukumar ta CNDH.
Alhaji Mustapha kadi Oumani shugaban rukunin wasu kungiyoyin fararen hullar CODDAE ne:

Ya ce "Wannan abin da suka yi abin yabo ne tunda sun fada wa shuwagabanni gaskiya to bamu sani ba ko yanzu za'a aiki da abinda suka fadi shi ne fatarmu".

Sauti da bidiyo akan labarin