1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddamar zaben fidda gwani a Zamfara

October 4, 2018

An shiga yanayi na takun saka tsakanin gwamnan jihar Zamfara da shugaban kwamitin da uwar jam'iyyar APC ta kasa ta aike zuwa jihar dan gudanar da zaben dan takarar gwamnan jihar wanda aka gudanar Laraba kuma aka soke.

https://p.dw.com/p/35ym6
Nigeria Vorwahl im Bundesstaat Zamfara
Hoto: DW/Y.I. Jargaba

An dai ci gaba da karbar sakamakon zaben duk kuwa da sokewa da kwamitin na kasa ya yi gami ma da uwar jam'iyyar APC ta kasa, dama dai tun bayan furta soke sakamakon zaben, Gwamna Abdul-aziz Yari Abubakar na jihar ta Zamfara ya ce maganar zabe tana nan daram dam babu fashi, don haka a ci gaba da zabe a yi watsi da batun sokewar da wakilin uwar jam'iyya ya yi.

Hakan kuma ta kasance domin kuwa an amshi sakamakon zaben kananan hukumomi hudu ana cigaba da dakon sauran goma. Ra'ayoyin wasu 'yan Jihar sun bambamta inda wasu ke ganin bai kamata ma gwamnan ya ki mutunta wakilcin uwar jam'iyyar ta kasa ba don kuwa shima a karkashin shugabancin jam'iyyar ta APC na kasa yake. Wasu kuwa na cewa gwamnan na kan bisa turba.

Ko yaya wadannan 'yan takara suka ji game da wannan mataki duk kuwa da kwamitin ya ba da shelar soke zaben? Sanata Kabir Garba Marafa na daga cikin masu neman tsayawa takarar gwamnan jihar ya ce kalaman na gwamnan ya nunar da cewa akwai kama karya ya kamata gwamnan ya ajiye mukaminsa ma.

Dr Abdu A. Fari shine ya shelanta soke zaben a jiya sakamakon wasu dalilai da suka hada da tada hankalin al'umma da kwace kayan zabe inda aka samu wasu jami'ai na gwamnati na cike takardun kuri'a ba bisa ka'ida ba.

Yanzu dai abun da ake jira shi ne ko uwar jam'iyya ta kasa za ta amince da sakamakon zaben.