Takaddama kan kudaden da Jonathan ya kashe a yakin neman zabe | Siyasa | DW | 20.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Takaddama kan kudaden da Jonathan ya kashe a yakin neman zabe

Jam'iyyar PDP na fuskantar zargi na almubazzaranci da dukiyar kasa wajen yakin neman zaben shugaba mai barin gado Goodluck Jonathan.

Kama daga malaman addini ya zuwa sarakuna da ma masu takama da sana'a ta siyasa dai, hadarin Naira da Dalar Amirka dai sun yi ruwan da babu irinsa a biranen Legas da Abuja, da suka zamo matattara ta jami'ai na gwamnatin kasar da ke barin gado kafin zabe.

To sai dai kuma duk da asarar kuri'ar da ma damar sake mulkin, tana shirin barin baya ga kura a kasar inda wata kafar labarai ta ruwaito kisan akalla Trilliyan na Naira har kusan biyu a kokari na sauyin ra'ayin a bangaren na Jonathan.

Sabon adadin da ke zaman kusan rabin kasafin kudin Najeriya na shekara dai ya kafa tarihin wandakar da babu irinta cikin tarihin siyasar kasar na shekaru 50 da doriya.

Sama da fadi da kudin kamfen

Jaridar dai ta ce tuni shugaban da ke shirin barin gadon ya nemi awo amai na kudaden da mafi yawansu suka kare a aljihun na masu siyasar maimakon 'yan zaben da ma ragowa na ayyukan da aka tsara batarwa.

Matsayin kuma da daga dukkan alamu ya ta da hankali a cikin fadar da ta dauki lokaci tana fadin an yi karin gishiri da suga da nufin tabbatar da bacin suna ga shugaban a fadar Farfesa Rufa'i Alkali da ke zaman babban mashawarci na siyasa ga Jonathan kuma daya a cikin jigon yakin tabbatar da sake zaben nasa.

Bata suna da neman yin bita da kulli

Kokari na binta da kulli ko kuma kokari na kai kare ga mayanka dai jam'iyyar PDP da ma shi kansa offishi na yakin neman zaben shugaban kasar dai sun bayyana Naira milliyan dubu 21 a matsayin gudummowar da suka kai ga tarawa da nufin yakin, kafin a kalli bushashar da ta dauki salon wasoso sannan kuma ta kare bata zuciya.

Facaka da bushashar kuma da a tunanin Dr Nazifi Darma da ke zaman masanni na tattalin arzikin kasar ke neman tabbatar da hasashe na kafar.

Abun jira a gani dai na zaman mafita ga masu mulkin na Abuja da ke cikin akuba ta asarar zabe sannan kuma ke shirin fuskantar zargin almubazzaranci da dukiyar al'umma ta kasa.

Sauti da bidiyo akan labarin