Taimakon wadanda ambaliya ta shafa | Siyasa | DW | 19.07.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taimakon wadanda ambaliya ta shafa

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce an dauki matakan taimako da sake gina wurare, kwanaki bayan da mumunan ambaliyar ruwa ta tagaiyara yammacin kasar.

Deutschland Unwetter in Rheinland-Pfalz | Malu Dreyer und Angela Merkel

Angela Merkel tare da Malu Dreyer a yayin da suka ziyarci wuraren da ambaliya ta shafa

Shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel ta ce samar da kudin sake gina yankunan na zama abin da gwamnatin tarayya za ta mayar da hankali, ganin irin matsalolin da mutanen yankunan da aka samu ambaliyar. Daya daga cikin wuraren da shugabar gwamnatin ta kai ziyarar shi ne garin Schuld ga kuma abin da atke cewa bayan gani da ido irin asarar da aka samu sakamakon wannan ambaliyar ruwa. "Na zo nan yau musamman garin Schuld tare da gwamna, domin bayyanawa karara cewa mu a gwamnatin tarayya muna son sanin hakikanin abin da ya faru, dole na ce yanayin abin tsoro ne. Abin girgiza. Zan iya cewa abin ya wuce lamar bala'i da Jamusawa suka sani."

Ta kuma yaba wa masu aikin ceto kan irin kokarin da suka yi cikin yanayi mai tsauri. Tuni mazauna yankunan da aka samu wannan ambaliyar suka bayyana halin da suka samu kansu da kuma abin da suke gani a matsayin makoma a gare su. "Na tashi kimanin karsfe 11 na dare na ji cikin ruwa wanda ya kai mita 20 lokacin da na sauka daga kan gado. Na tashi matata na fita da ita waje. A lokacin ruwa ya kai gwiwa. Na koma daki domin kwashe takardunmu masu muhimmanci. Na nji mamakin irin yadda ruwan cikin hanzari ya mamaye ban taba fuskantar irin wannan yanayin ba." Ban san abin zan yi ba. Ina da yara hudu. Wannan bala'i ne. Babu wanda ya san lokacin da zai dauka kafin sake gina nan wurin, shekara daya ko biyu. Kuma babu aiki."

Nach dem Unwetter in Rheinland-Pfalz

Mutane na rage ruwa daga gidajensu

Yayin zirayar shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel ta bukaci ganin nunka kokarin da ake yi a bangaren siyasa domin dakile matsalolin da sauyin yanayi suka haifar kamar wannan ambaliyar ruwan wadda ta halaka mutane 180 a kasashen yammacin Turai "Ambaliya guda daya ba za ta nuna sauyin yanayi ba, amma idan muka duba abubuwan da suke faruwa a shekarun da suka gabata, za a iya cewa ana samun bala'i a kai- a kai, domin haka sai mun kara himma da azama."

Ko da yake ruwan sama ya tsaya a yankunan da aka samu ambaliyar ruwa na Jamus, da Beljiyam gami da Holland, amma ana ci gaba da zabga ruwa sama a wasu kasashe na yammaci da tsakiyar Turai. Tuni gwamnatin jihar North Rhine Westphalia Armin Laschet wanda kuma yake fata ya gaji kujerar shugabar gwamnati bayan zaben watan Satumba mai zuwa na jam'iyyar CDU mai mulki, ya shiga tsaka mai wuya sakamakon ganin sa yana dariya bayan ziyarar wasu wuraren da aka samu ambaliyar ruwa a jihar. Gwamnan ya ce rashin fahimat ce lokacin da aka ga yana dariya yayin da shugaban kasar Jamus President Frank-Walter Steinmeier yake ziyara tare da rakiyar gwamnan.