1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin Ursula von der Leyen a takaicce

Strack Christoph AS
July 3, 2019

Shugabannin Kungiyar EU sun zabi ministar tsaron Jamus Ursula von der Leyen a matsayin shugabar kungiyar bayan wani zama da suka yi, mutane da dama dai sun yi mamakin wannan nadi.

https://p.dw.com/p/3LWQs
Ursula von der Leyen sabuwar shugabar hukumar gudanarwa ta EU
Ursula von der Leyen sabuwar shugabar hukumar gudanarwa ta EUHoto: picture alliance/dpa/M. Skolimowska

An haifi Ursula von der Leyen kimanin shekaru sittin da suka gaba a birnin Brussels na Kasar Beljiyam kuma ita da mahaifanta wadanda Jamusawa ne sun zauna a birnin na Brussels har lokacin da ta cika shekaru 13 da haihuwa. Ta fuskar ilimin boko dai von der Leyen ta karanci tattalin arziki kafin daga bisani ta sake komawa makaranta don yin karatun zama likita kuma bayan ta kammala shi ne ta fara harkoki na siyasa inda ta shiga jam'iyyar nan ta CDU a shekarar 1990. Bayan shigarta harkokin siyasa sosai ta rike mukamai da dama ciki kuwa har da 'yar majalisar ta jiha a Jihar nan ta Lower Saxony a shekarar ta 2003 kafin daga bisani kuma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta nadata minista da ke kula harkokin iyali da lafiya sai kuma daga bisani ta kasance ministar harkokin tsaro wadda ita ce mace ta farko da aka nada kan wannan mukami kuma har yanzu tana rike da shi. Da dama na kallonta a matsayin wadda ta kawo sauye-sauye ciki kuwa har da batun sake fasalta rundunar sojin Jamus da kuma kokari wajen amfani da sojin ruwanta kan batun 'yan gudun hijira. Da yawa dai a nan Jamus da ma wasu kasashen Turai na daukar Ursula von der Leyen a matsayin mace mai jajircewa kan aikinta da kyakkyawar mu'amala a tsakanin abokanta 'yan siyasa. Nan gaba kadan ne dai 'yan majalisar dokokin Turai za su yi zama na musamman domin kada kuri'a amincewa da nadin nata ko akasin haka.