Taba Ka Lashe: 09.08.2017 | Al′adu | DW | 10.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Al'adu

Taba Ka Lashe: 09.08.2017

Musulmi 'yan yawon buden ido sun fi sha'awar zuwa wurare da ke da tanade-tanade irin na addininsu, musamman a Turai.

Wani rukuni na masu matsakaicin karfi na karuwa a sassa dabam-dabam na kasashe masu tasowa, wanda ke kawo canje-canje masu tarin yawa kan yadda mutane ke amfani da lokacinsu na hutu, inda da yawa ke zaban zuwa kasashen ketare don yin hutu na shekara.

A dangane da haka su ma Musulmi 'yan yawon buden ido sun fi sha'awar zuwa wurare da ke da tanade-tanade irin na addininsu, musamman a Turai da ake wa lakabi da Halal Holidays.

Sauti da bidiyo akan labarin