Taba Ka Lashe: 07.02.2018
February 10, 2018Talla
Yayin da aka fatattaki kungiyar nan ta masu kaifin kishin addinin Musulunci wato IS daga yankin nan da ta kira Daularta, da yawa daga cikin mayakanta na neman wuraren da za su tsere. Ga wasu a cikinsu tudun mun tsira shi ne dawowa gida nahiyar Turai, kasancewa daga cikin mayakanta akwai wadanda suka fito daga kasashen Turai. Shin wane irin kalubale hakan ke da shi a kasashensu na asali? Muna dauke da karin bayani a shirin.