1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Suka ga matakin EU game da rikicin Ukraine

putuiMarch 19, 2014

Har yanzu Rasha na shan suka da kaukkausan lafazi daga kasashen yamma dangane da matsayinta a kan yankin Kirimiya. Sai dai su ma kasashen yamma da na su laifi.

https://p.dw.com/p/1BSYJ
Krim Krise Marinestützpunkt 19.03.2014 Sewastopol
Hoto: Reuters

Tuni kuwa kungiyar tarayyar Turai da kuma gwamnatin Amirka suka sanya wa Rashar takunkumi bisa goyon bayan da take nuna wa al'ummar yankin na Kirimiya da suka kada kuri'ar amincewa su hade da Rasha. Sai dai wasu na ganin su ma kasashen yamma da na su laifin a rikicin na Ukraine da ma Kirimiya.

Kasashen yamma na fassara matakin hadewa da Rasha da yankin Kirmiya yayi da cewa gwamnatin Mosko ce ta mamaye wannan yankin tsibiri. Sannan kuri'ar raba gardamar da al'ummar yankin wanda akasarinsu masu magana da harshen Rashanci ne, suka kada a karshen mako, haramtacciya ce wadda ba za su taba amincewa da ita ba. Shin ko ana iya cewa shugaban Rasha Vladimir Putin ya tabka babban kuskure ke nan bisa matakin da ya dauka a Kirimiya? Günter Verheugen shi ne tsohon kwamishinan tarrayar Turai da ke kula da batun fadada kungiyar da kuma manufofinta na masana'antu, ya ce Putin ya san abin da yake yi.

EU Kommissar Günter Verheugen
Günter Verheugen tsohon kwamishina na EUHoto: AP

Rashin duba muradun Rasha da kasashe makwabta

"Yana kare wasu muradu ne da yanzu Amirkawa ke cewa daidai ne wato muradun tsaron kasar Rasha. Da ya yi kyau in da tun farko an nemi yin tattaunawa da Rasha game da batun na Ukraine tare da la'akari da bukatunta na tsaro. Amma sai bayan da rikicin ya kai kololuwarsa aka fara tuntubar Rasha."

Verheugen ya kara da cewa kuskuren da tarayyar Turai ta tabka game da manufarta da ta shafi Ukraine da ma kasashe makwabta a wannan yanki shi ne, cusa musu kwadayin shigar da su cikin kungiyar EU ba tare da tattauna da manyan kasashe kuma masu muhimmanci a wannan yanki ba. Matakin da Johannes Posth masanin dokokin kasa da kasa kuma memba na wata kungiyar Jamus da Ukraine ya ce babban kuskure ne daga bangaren EU.

"Kungiyar EU ta gaza a fannin diplomasiyya saboda karancin shiri a tattaunawar shigar da Ukraine da kuma batun tattalin arziki musamman wanda ya shafi Rasha. Amma kuma babban kuskure shi ne rashin shigar da Putin cikin shirye-shiryen."

Gungun masu tsattsauran ra'ayin kishin kasa

Wani batun da ya dauki hankali shi ne kasancewa a cikin sabbin hukumomin Ukraine akwai masu matsanancin ra'ayin kishin kasa ne wadanda kuma ke da tsattsauran ra'ayin kyamar Rasha, Yahudawa da kuma kasar Poland wadanda kuma har wa yau ke son Ukraine ta mallaki makaman nukiliya, inji Günter Verheugen tsohon kwamishinan fadada kungiyar EU.

Ukrainischer Übergangspräsident Alexander Turtschinow vor dem Parlament in Kiew 15.03.2014
Alexander Turtschnov shugaban rikon kwaryar UkraineHoto: Imago

"Wasunsu ba su da burin hadewa da tarayyar Turai, suna daukar kungiyar a matsayin wata hadaka da ba za ta yi karko ba, wadda ko ba dade ko ba jima za ta wargaje. A cikin tarihin Turai mun shaida yadda irin wannan hadin kai da masu matsanancin ra'ayi ya janyo mana koma baya. Bai kamata mun manta da wannan ba."

Yanzu haka dai kungiyar tarayyar Turai da kuma Amirka sun sanya wa Rasha da wasu daidaikun 'yan Ukraine takunkumai. Sai dai Günter Verheugen ya nuna damuwa da yadda a kullum matakan jan kunne ke kai su su baro musamman daga yin karatun mun natsu a kan ainihin abubuwan da suke cimmawa, wato bin kyawawan manufofi na huldar dangantaka da samun fahimtar juna. Da zaran an fara daukar irin wadannan matakan da wuya a iya komawa ga tsohuwar dangantaka.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar