Yaushe za a kawo karshen yakin Sudan?
November 7, 2025
Kwararru dai na ganin babu tabbacin rundunar RSF a shirye take ta aiwatar da sulhun, tare da yin gargadin cewa mayakan na shirin kai munanan hare-hare da nufin kwace iko da birnin el-Obeid da ke kudancin kasar. Gwamnatin da sojoji ke goyon baya, ba ta amsa tayin na al'ummomin kasa da kasa karkashin jagorancin Amurka ba.
Yakin sama da shekaru biyu
Abubuwa masu fashewa sun yi bindiga a Khartoum babban birnin kasar da ke karkashin ikon sojojin gwamnatin. Tun a watan Afrilun 2023 ne, yaki ya sake barkewa a Sudan tsakanin sojojin gwamnatin Janar Abdel Fattah al-Burhan da mayakan RSF karkashin jagorancin tsohon mataimakinsa Mohammed Hamdan Daglo.
A hannun guda Majalisar Dinkin Duniya ta zargi Hadaddiyar Daular Larabawa da bai wa mayakan na RSF makamai, zargin da Daular Larabawan ta yi ta musantawa. A hannu guda kuma, Saudiyya da Masar da Turkiyya da Iran na tallafawa sojojin gwamnati.
Yunkurin samar da zaman lafiya
A yanzu Amurka da Saudiya da Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Masar na neman a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, a yakin da ya tarwatsa sama da mutane miliyan biyu tare da haifar da mummunan yanayin agajin jin-kai.