Amurka na son kin amince wa zaman sojojin ketare a Sudan
November 6, 2025
Amurka ta yi barazanar kin amincewa da tsawaita wa'adin rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a yankin Abyei, yankin da ke cikin rikici tsakanin Sudan da ke fama da yakin basasa da kuma makwabciyarta Sudan ta Kudu, muddin dai bangarorin biyu suka ki amincewa da aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya ta shekarar 2011.
Yayin zaman kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da aka gudanar a ranar Laraba, jakadan Amurka a Majalisar, Mike Waltz, ya bayyana sharuddan da kasarsa ta gindaya kafin ta goyi bayan tsawaita wa’adin rundunar ta Majalisar Dinkin Duniya da ke Abyei, wato UNISFA, wadda wa’adinta ke karewa a ranar 15 ga Nuwamba.
Waltz ya shaida wa kwamitin cewa ya zama wajibi yanzu Sudan da Sudan ta Kudu su cika alkawuran da suka dauka bisa yarjejeniyar zaman lafiya ta 2011 da kuma tanadin UNISFA, domin samun goyon bayan Amurka wajen tsawaita aikin rundunar.