1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan: An amince da kai agajin jinkai

May 12, 2023

Bayan tattaunawa ta mako guda a audiyya, wakilan bangarori masu gaba da juna a Sudan sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar tsagaita hare-haren na dan wani lokaci a nan gaba.

https://p.dw.com/p/4RF8F
Hoto: Mohamad Ali Harissi/AFP

Bangarori masu gaba da juna a Sudan, sun amince da bai wa fararen hula kariya tare da ba da damar kai kayayyakin jinkai a yankunan da ke bukatar haka a kasar.

Sai dai bangarorin na Sudan da ke fadin hakan a wannan safiya ta Juma'a, sun ki amincewa da batun tsagaita bude wuta a tsakaninsu.

Bayan tattaunawa ta mako guda a birnin Jeddah na kasar Saudiyya, wakilan gwamnati da kuma rundunar mayakan ko ta kwana ta RSF sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar tsagaita hare-haren na dan wani lokaci nan gaba.

Wani babban jami'in ma'aikatar kula da harkokin wajen Amurka, ya ce abun da ya tabbata a yanzu, shi ne sasanta wannan rikici na Sudan zai dauki lokaci ga dukkan alamu.

Ministan harkokin wajen Saudiyya Faisal bin Farhan ya ce tattaunawa kan kare fararen hula da aka cimma dai shi ne mataki na farko, inda saura kuwa ke tafe.