Somamen jami′an tsaro a yammacin Jamus | Labarai | DW | 22.03.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Somamen jami'an tsaro a yammacin Jamus

Hukumomin Jamus sun sanar da capke mutane 11 a wani somame da aka kai a kan wasu gungun mutane da ake zargi da shirin kai harin ta'addanci da motoci da makamai.

Kampanin dillancin labaru na Jamus na DPA ya ruwaito cewar, masu shigar da kara a birnin Frankfurt sun shaidar da cewar, manufarsu ita ce su kai hare-hare a wurare daban daban.

Bayanai sun ce manyan wadanda ake zargin wasu 'yan uwa ne masu shekaru 31 daga birnin Wiesbaden da wani dan shekaru 21 daga Offenback da ke kusa da Frankfurt. Jami'an tsaro wajen 200 ne suka kai somamen.