1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaAfirka

Matasan Sokoto da TikTok

May 21, 2024

A Najeriya yayin da hukumomin kasar suka bukaci kamfanin TikTok da ya soma sanya idanu kan abubuwan da ‘yan Najeriya ke wallafawa a shafin, domin kaucewa kalaman batanci da yada karya.

https://p.dw.com/p/4g6lh
Manhajar I TikTok
TikTokHoto: Mario Tama/Getty Images

Matasa da dama a Najeriya na bayyana irin yadda wannan shafi na TikTok ke burge su, dangane da irin abubuwan da ake wallafawa, galibi na matasa, to amma kuma duk da irin karbuwa da kuma yadda ake ganin matasa na sheke ayarsu a wannan shafi na TikTok, lamarin na daukar hankalin masana zamantakewar bani adama, da hukumomin Najeriya, dangane da tantance abubuwan da matasan za su rika wallafawa wanda bai sabawa duk wani addini ko al'ada irin ta ‘yan kasar ba.

Karin Bayani: Matashi ya kunna wa masallaci wuta a Kano

A Najeriya dai alkaluma sun nuna a wannan shekara ta 2024 masu amfani da shafin TikTok a fadin kasar sun kai mutane miliyan 23.84, sai dai irin yadda ake hasko matasa maza da mata na raye-raye da sakin tsiraici, na bakanta ran mutane da dama musamman masu fafatukar gyaran tarbiyyar matasa a cikin kasar.