1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matashi ya jikkata mutane a masallaci

Abdul-raheem Hassan
May 15, 2024

Limamin masallacin da wani mutum ya kai hari a jahar Kano ya rasu da wasu mutane guda biyu, akjwai karin mutane da dama da ke kwance a asibiti.

https://p.dw.com/p/4ftjq
Symbolbild Nigeria Angreifer befreien tausend Häftlinge aus Gefängnis
Hoto: Olamikan Gbemiga/AP Photo/picture alliance

Rahotaanni daga jihar Kano da ke arewacin Najeriya na cewa akalla mutane 24 sun jikkata, ciki har da wasu yara kanana guda hudu a lokacin da wani mutum ya cinna wuta a cikin wani masallaci bayan sallar asuba a unguwar Gadan.

'Yan sanda sun sun tabbatar da kama matashi mai shekaru 38 wanda ya tabbatar da kai harin tare da cewa ya aikata hakan ne saboda an bata masa rai a gidansu.

Binciken farko na 'yan sanda ya nuna cewa matashin ya yi amfani da gas wajen haddasa fashewa a cikin masallacin, sai dai hukumomi sun ce ana cigaba da gudanar da bincike.