1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Ukraine sun yi wa dakarun Rasha kawanya

October 1, 2022

Sa'o'i da sanar da kwace yankunan kasar Ukraine da Rasha ta yi, sojojin Ukraine sun kewaye wasu dubban mayakan gwamnatin Rasha a gabashin Donetsk.

https://p.dw.com/p/4Hd8s
Ukraine-Krieg Mariupol | Gefangennahme ukrainische Soldaten am Stahlwerk Azovstal
Hoto: Russian Defense Ministry/AP/picture alliance

Gwamnatin Ukraine ta ce ta yi wa dubban dakarun Rasha kawanya a kusa da wani yanki da ke cikin garuruwa hudu da Shugaba Putin ya bayyana maida su cikin Rasha.

A jiya Juma'a ne dai shugaban na Rasha ya yi bikin shigar da yankunan cikin kasarsa, abin da ya fuskanci suka musamman daga kasashen yamma.

Garuruwan dai da Rasha ta karbe daga Ukraine, su ne Lugansk da Donetsk da Kherson da kuma Zaporizhzhia.

A wannan rana ta Asabar ne dai sojojin Ukraine din suka yi wa garin Lyman na yankin Donetsk kawanyar, inda ake da dakarun Rasha kimanin dubu biyar.