Sojojin Najeriya sun tsere cikin Kamaru | Labarai | DW | 26.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Najeriya sun tsere cikin Kamaru

Yanzu dai ta tabbata dimbin sojojin Najeriya sun gudu daga Najeriya sun shiga Kamarun bisa tsira da rayukansu bayan gumurzun da suka yi da Boko Haram

Ma'aikatar tsaron Kamaru ta tabbatar da cewa kimanin sojojin Najeriya 500 suka tsere wa fada da Boko Haram suka shiga makobciyar Najeriya wato kasar Kamarun. Ma'aikatar tsaron kasar ta a Yaounde ta ce yanzu an tsugunar da sojojin a wata makaranta da ke kilo mita 80 daga kan iyakar Najeriya. Daga karshe ita ma rundunar sojan Najeriya ta yarda cewa e lallai sojojinta sun gudu daga fagen daga, amma ta ce hakan dabara ce ta sake damaran yaki. Kungiyar Boko Haram dai ta karbi birane da dama a 'yan kwanannan, a jihohin da yanzu haka sojojin Najeriya ke iko da su a karkashin dokar ta-baci. Kungiyar dai tana cewa wai nufinta shi ne kifar da gwamnantin Tarayya ta kafa daular musulunci.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu