Birgediya Janar Sani Usman Kuka-Sheka mai magana da amadadin rundunar, ya ce dakarun kasar sun yi nasarar kashe kusoshin kungiyar biyar tare da jikkata wasu mambobin ta Arewa maso gabashin Najeriya.
Wannan ikirarin na sojojin Najeriya na zuwane mako guda bayan da wasu 'yan kungiyar ta Boko haram kusan 70 suka mika wuya ga gwamnatin kasar, bayan wasu jerin somame da sojojin ke kaddamarwa.
Kungiyar Boko Harama dai ta zama barazana ga rayuwar fararen hula da ke yankin Arewa maso gabashin Najeriya, da ma kasahen Nijar da Chardi da ke makobtaka da kasar. To sai dai haryanzu sojojin Najeriya na kan bakansu na ganin sun murkushe ayyukan kungiyar baki daya, inda a yanzu ake saura kiris na cikar wa'adin kwanki 40 na kamo shugaban kungiyar Abubakar Shekau.