Sojoji sun gano gawawwaki a Damasak | Labarai | DW | 21.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojoji sun gano gawawwaki a Damasak

Sojojin Nijar da na Chadi sun gano wasu gawawwaki masu yawa a garin Damasak na jihar Borno da ke Tarayyar Najeriya bayan sun kwato garin a hannun 'yan Boko Haram

Dakarun kasashen Nijar da Chadi da suka kwato garin Damasak na jihar Bornon Najeriya daga hannun mayakan Boko Haram, sun ce sun ga wasu gawawwakin mutane masu yawa a yashe karkashin wata gadar dake yankin na Damasak, da suka yi imanin cewa mayakan Boko Haram ne suka halaka su.

Kamar dai yadda wani sojan Chadi ya shaidar, ya ce sun ga akalla gawarwakin mutane 100 a gadar, da wani daga cikinsu da aka yiwa yankan Rago.

Sai dai alamun da ke wajen na nunin cewa, wannan danyen aikin ya dan kwana biyu saboda irin bushewar da gwawarwakin suka yi.

Daga cikin gawawwakin harma da ta wani limamin garin.