1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojin Najeriya sun dakile harin Boko Haram

December 7, 2018

Mayakan kungiyar mayakan Boko Haram sun kai wasu sabbin hare-hare kan sojoji da ke Bama da Rann na jihar Borno a arewacin Najeriya.

https://p.dw.com/p/39ejD
Boko Haram
Hoto: Java

Rahotannin da ke fitowa daga Najeriya, na cewa mayakan Boko Haram sun kai wani sabon hari a sansanin soji da ke garin Bama cikin daren da ya gabata, bayan wani makamancinsa da suka kai garin Rann a jiya Alhamis.

Bayanai dai sun tabbatar da cewa dakarun Najeriyar sun maida martanin kan mayakan na Boko Haram da suka shiga yankunan cikin jerin gwanon motoci da ma damara dauke da muggan makamai.

Babu dai cikakkun bayanai kan adadin wadanda suka mutu ko jikkata a hare-haren biyu saboda matsalar sadarwa.

Amma akwai wasu ruwayoyin da suka ce babu wani jami'in soji da aka rasa a hare-haren.

Hakan kuwa na zuwa ne a dai dai lokacin da rundunar sojin Najeriya ta sanar da sauye-sauyen jagororin rundunonin da ke yaki da ta’addanci musamman a shiyar arewa maso gabashin kasar.