1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojin Jamus za su ci gaba da zama a Afghanisan

Ahmed Salisu
February 23, 2021

Ministocin Tarayyar Jamus sun ce za su sahalewa dakarun kasar su ci gaba da yin aikin a kasar Afghanistan har zuwa ranar 31 ga watan Janairun shekarar 2022.

https://p.dw.com/p/3plY8
Afghanistan Bundeswehr NATO Resolute Support Mission
Hoto: picture-alliance/dpa/S. Mustafa

Ministar tsaron kasar Annegret Kramp-Karrenbauer ce ta ambata hakan a yau a wani zama da suka yi gabannin karewar wa'adin da aka debawa sojin Jamus din na yin aiki a Afghanistan din wanda ke cika a karshen watan gobe.

Kramp-Karrenbauer ta ce janye dakarun daga kasar ta Afghanistan a wannan lokacin zai jawo nakasu ga kokarin wannzar da zaman lafiyar da ake yi tsakanin gwamnatin kasar da 'yan Taliban.

Kimanin sojin kasar ta Jamus dubu da dari uku ne yanzu haka ke aiki a kasar ta Afghanistan don wanzar da zaman lafiya.