Siriya: Putin ya tattauna da Macron | Labarai | DW | 09.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Siriya: Putin ya tattauna da Macron

Shugaba Vladimir Putin na Rasha da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron sun yi wata ganawa a wannan Juma'ar ta wayar tarho kan halin da ake ciki a Siriya da kuma batun kasar Ukraine.

Emmanuel Macron und Wladimir Putin Bildkombo Kombi-Bild (picture-alliance/dpa/Liewig/Klimentyev)

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Wladimir Putin na Rasha

Tattaunawar ta shafi batun shirin ziyarar da shugaban na Faransa zai kai zuwa Rasha, inda zai halarci babban zaman taro kan tattalin arziki da zai guda a birnin Saint-Pétersburg na kasar ta Rasha daga ranar 24 zuwa 26 ga watan Mayu a cewar fadar shugaban kasar ta Rasha ta Kremlin cikin wata sanarwa da ta fitar a yau din.

Bangarorin biyu na Rasha da Faransa sun sanar da bukatunsu na ganin an ci gaba da tattaunawar da ake ta neman sulhu a rikicin Siriya, inda suke ganin ya kyautu a karfafa hulda tsakanin kasashen biyu wajen walwale wannan rikici. Daga bisani shugabannin biyu sun kuma tattauna batun kasar Ukraine, inda suka nuna mahimmancin aiwatar da yarjejeniyar nan ta zaman lafiya da aka cimma ta birnin Minsk da ke da burin kawo karshen rikicin gabashin kasar Ukraine.