Siriya: Neman hanyoyin warware rikici | BATUTUWA | DW | 05.03.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Siriya: Neman hanyoyin warware rikici

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da takwaransa na Turkiyya Recep Tayyip Erdogan na tattaunawa da nufin neman mafita kan rikicin yankin Idlib da ke Arewa maso Yammacin kasar Siriya, rikicin da ya ke kara rincabewa.

Russland Moskau | Recep Tayyip Erdogan und Vladimir Putin

Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya da takwaransa na Rasha Vladimir Putin

Yankin na Idlib dai na zaman tungar karshe da 'yan tawayen Siriya ke da karfi. Da yake jawabin bude taron da aka yada a gidan talabijin, Shugaban Turkiyya Racep Tayyip Erdogan ya nunar da cewa ya san a yanzu baki dayan idanun duniya na kansu. Ya kara da cewa matakin da za su dauka bayan kammala taron zai shawo kann matsalar da yankin da ma kasashensu ke ciki. Wannan tattaunawa dai na azuwa ne a daidai lokacin da ake tsaka da zaman dar-dar, dangane da yiwuwar barkewar yakai a fakaice tsakanin Turkiyya da ke taimakawa 'yan tawayen Siriya da kuma Rasha da ke taimakwa gwamnatin Siriyan karkashin jagorancin Bashar al-Assad. Rahotanni sun nunar da cewa dakarun kasar Turkiyya da dama sun rasa rayukansu a wannan arangama, tun bayan da Turkiyyan ta tura su zuwa yankin na Idlib.

Syrien Zerstörung von Wohngebieten und Infrastruktur in Idlib

An ragargaza yankin Idlib na Siriya

Tun kafin gudanar da wannnan taron dai, shugabannin biyu sun nuna aniyarsu ta yin duk mai yiwuwa domin ganin ba a samu  yin fito na fito da juna a yankin na Idlib ba, batun da shugaban Rasha Vladmir Putin ya kara jaddada shi a yayin wannan ganawar bayan da ya sake jajantawa Turkiyyan kan kashe sojojinta 33 da akayi a harin da ake cewa sojojin Siriya ne suka kai musu a arewacin kasar ta Siriya, inda Erdogan a nasa bangaren ya ce sa-in-sar da ke tsakanin kasashen biyu kan yankin Idlib ba za ta kawo tangarda ga kakkarfar alakar da ke tsakanin kasashen biyu a bangarori mabanbanta ba.

Sauti da bidiyo akan labarin