Shugabar gwamnatin Jamus ta karye | Labarai | DW | 06.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugabar gwamnatin Jamus ta karye

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta fadi yayin wasa a kankara a kasar Switzerland

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta fadi ta karye a mara, yayin da take wasa a kan kankara cikin yankin kasar Switwerland.

Kakakin shugabar Steffen Seibert ya ce ta fadi lokacin da take wasan tsakanin kasashen biyu, kuma an soke duk wasu ayyuka da aka tsara za ta gudanar. Likitoci sun ce Merkel za ta kwashe kimanin makonni uku tana hutawa, inda take tafiya da taimakon sanda.

Amma duk da wannan hali, Shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel, za ta jagoranci zaman majalisar gudanarwa na ministoci da zai gudana ranar Laraba mai zuwa.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal