1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yoweri Museveni: Mulkin mutu ka raba?

May 12, 2021

Tsarin mulkin mutu ka raba na Yoweri Museveni da kuma batun take hakkin dan Adam daga gwamnatinsa, na kara janyo cece-kuce daga kasashen ketare.

https://p.dw.com/p/3tJMF
Uganda Kampala | Erneute Amtseinführung | Yoweri Museveni
Yoweri Museveni ya yi rantsuwar kama mulki a wa'adi na shidaHoto: Lubega Emmanuel/DW

A Larabar  wannan makon shugaban na Yuganda Yoweri Museveni ya sha rantsuwar kama aiki a wani sabon wa'adin mulki na shekaru biyar. Da dama dai na ganin da wuya shugaban ya sauya irin matsayin da yake kai na mulkin kama-karya da ma irin yadda cin hanci da rashawa ya yi kaka-gida a kasar. Bayan ayyana shi a wanda ya lashe zabe, ya samu damar yin mulki a wa'adi na shida tun bayan da ya karbe madafun iko kimanin shekaru 35 da suka gabata. Ana ganin cewa, abokansa na kasashen Yamma na taka tsan-tsan wajen bata ran gwamnatin da ta taimaka wajen daidaita al'amura a yankin.

Karin Bayani: Take hakkokin 'yan adawa a Yuganda

Sai dai mutane da dama a kasar na ganin rashin dacewarsa wajen ci gaba da mulki. Sai dai mutane kamar Teddy Atim na da tunanin akasin haka. A zantawarta da DW, Teddy ta ce mutane da dama na kyautata masa zato a wannan sabon wa'adin mulkin nasa, musamman ma ta fuskar aiyyukan raya kasa. Shi ma dai Godfrey Kiwanda da ke zaman mukaddashin shugaban jam'iyyar NRM ta Shugaba Museveni cewa ya yi, al'ummar kasar na yi wa shugaban kyakkyan fata, domin a wannan jikon ya daura damarar fitar da 'yan kasar daga kangin talauci da ma inganta rayuwar al'ummar da yake mulka.

 Flüchtlinge aus dem Südsudan beim Unterricht  in den Flüchtlingslagern Parolinya und Ofua
Yuganda: Matsuguni ga 'yan gudun hijira daga makwabtaHoto: DW/E. Lubega

To sai dai a daura da wadannan kalamai na Mr. Kiwanda da sauran magoya bayan shugaban na Yuganda, masanin tarihi a jami'ar Makerere da ke kasar ta Yuganda, Farfesa Mwambutsya Mwebesa ya ce da wuya ta sauya zani a wannan sabon wa'adin na Museveni kasancewar an riga an dankwafe al'umma ta yadda ba za su iya kwatar 'yancinsu na siyasa ko ma 'yancin dan Adam kamar yadda yake a sauran kasashe ba.

Karin Bayani:Sojoji sun yi wa gidan Bobi Wine kawanya

Wani abu har ila yau da masana irinsu Farfesa Mwebesa ke nuna fargaba a kai shi ne, ci gaba da takure 'yan adawa da shugaban kasar zai rika yi ba tare da fuskantar wani kaluble ba walau daga cikin gida Yuganda ko kuma kasashen ketare. Masu sanya idanu kan abubuwan da ke kai-komo a kasar ta Yuganda, na ganin irin yadda shugaban ke ci gaba da jan zarensa ba tare fuskantar kalubale ba na da nasaba da irin yadda yake kula da 'yan gudun hijirar kasashe irinsu Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kongo da Sudan ta Kudu da ma sabon kawance da ya kulla da Chaina, wadda da wuya ta sanya masa ido a harkokinsa na cikin gida.