1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bobi Wine ya zame wa Yuganda ala-kakai

Mohammad Nasiru Awal MAB
January 10, 2020

Cikin hsarhin da ta yi jaridar Süddeutsche Zeitung wadda ta ce matashin nan dan salon wakar rap Bobi Wine ya zame wa manyan masu mulki a kasar Yuganda ala-kakai kasancewa yana samun nasara fiye da 'yan siyasa.

https://p.dw.com/p/3Vz9j
Uganda Kampala Festnahme Bobi Wine
Hoto: Getty Images/AFP/Stringer

Jaridar Süddeutsche Zeitung ta ce mawakin da sunansa na yanka shi ne Robert Kyagulanyi Ssentamu amma ake wa lakabi da Bobi Wine, ana kuma kiransa jagoran talakawa, kasancewa an haife shi ne a wata unguwar talakawa da ke Kampala babban birnin kasar, ya kuma tashi cikin talauci. A wakokinsa mawakin da ya rikide ya zama dan siyasa a Yuganda, ya fi mayar da hankali kan matsalar rashin adalci a zamantakewa da yawan cin hanci da rashawa da ya yi katutu tsakanin 'yan siyasa musamman Shugaba Yoweri Museveni, wanda tun a 1986 yake kan mulki da ake zargi da mulki irin na kama karya. Amma saboda wannan matsayi na mawakin da kuma kokarin hada kan matasa su yi zanga-zanga ana yawaita kama shi.

Isabel dos Santos: Attajira ko mai sama da fadi?

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta labarto cewa bayan da wata kotu a Luanda babban birnin kasar Angola ta dora hannu kan kadarorin Isabel dos Santos, yanzu 'yar tsohon shugaban kasar da ke zama mace mafi arziki a Afirka, ta bayyana hukuncin kotun da bita da kulli na siyasa da ya sabawa dukkan dokokin kasar.A shari'ar kan cin hanci da rashawa, ana zarginta da amfanin da kamfanin mai na kasar wato Sonangol da kamfanin lu'ulu'u na Sodiam wajen azurta kanta da kanta. saboda kotu ta neme ta da ta mayar wa kasar dala miliyan dubu 1.136. Jaridar ta ce wannan shari'ar ta nuna fili cewa ba wanda ya wuci sandar shari'ar ta buge shi a kasar da ke matsayi na biyu na arzikin man fetur a Afirka amma kuma ke fama da tabarbrewar tattalin arziki.

Angola l Isabel dos Santos - Gericht zieht Vermögen
'Yan tsohon shugaban Angola dos santos ta shiga tarkon kotuHoto: picture alliance/dpa/TASS/M. Metzel

Yaki da cin hanci gadan-gadan a Angola

Ita ma jaridar Neue Zürcher Zeitung ta yi tsokaci kan shari'ar tana mai cewa gimbiyar Angola za ta mayar da kadarorin da ta mallaka, sannan sai ta ci-gaba da cewa da gaske sabon shugaban kasar Angola Joao Lourenco yake wajen yaki da cin hanci. Ta ce kusan shekaru 40 Angola ta kasance karkashin mulkin wani iyali. Ta ce karkashin Shugaba Jose Eduardo dos Santos an raba muhimman mukamai ga dangi da abokai, da wuya a iya rarrabewa tsakanin baitul-malin gwamnati da kadarori na daidakun mutane. Babban misali na wannan tsari na zama Isabel dos Santos, 'yar tsoho shugaban, wadda aka kiyasce kadarorinta sun kai dala miliyan dubu 2.2. Sai dai yanzu da alamu abubuwa za su canja domin a farkon wannan shekara kotu a Angola ta bada umarnin kwace dukkan kadarorin Isabel do Santos mai shekaru 46, saboda zargin cin hanci da rashawa.

CAF Awards 2019
Sadio Mane ya zama gwanin kwallon kafa a Afirka da duniyaHoto: Reuters/A.A. Dalsh

 Sadio Mane: Gwarzon kwallon kafar Afirka

Za mu karkare da jaridar Süddeutsche Zeitung wadda ta yi tsokaci kan gwarzon dan kwallon kafar Afirka na 2019 da aka ba wa dan kasar Senegal mai kuma yi wa kungiar Liverpool ta Birtaniya wasa, wato Sadio Mane. Ta ce ko shakka babu Mane da ya zama gwarzon dan kwallon kafar Afirka na 2019, ya saamu lambar yabo ne da masharhanta da yawa ke ganin an dadada masa bayan da kiris ya gaza zama gwarzon dan kwallon kafar duniya na 2019.