Angola tana cikin kasashen Afirka kalilan da Potugal ta yi wa mulkin mallaka kafin boren da samun 'yanci a shekarar 1974.
Tun lokacin kasar ta tsunduma yakin basasa tsakanin MPLA da Agostinho Neto ke jagoranta zuwan lokacin da ya rasu a shekarar 1979. Jose Eduardo dos Santos ya dauki madafun iko a matsayin shugaban kasa, ya ci gaba da fafatawa da Jonas Savimbi jagoran Unita. Yakin ya kawo karshe lokacin da Savimbi ya mutu a shekara ta 2002 yayin fada da dakarun gwamnati.