1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan adawar Yuganda cikin matsi

Abdul-raheem Hassan LMJ
January 21, 2021

Kasashen duniya na zargin shugaban kasar Yuganda Yoweri Museveni ta take hakkin dan Adam. Wannan dai na zuwa ne bayan da rahotanni ke cewa har yanzu madugun adawar kasar Bobi Wine na karkashin daurin talala.

https://p.dw.com/p/3oFV4
Tansania Chato 2020 | Yoweri Museveni, Präsident Uganda
Shugaban kasar Yuganda Yoweri MuseveniHoto: Tanzania State House/Xinhua News Agency/picture alliance

Wannan dai na zuwa ne bayan da rahotanni ke cewa har yanzu madugun adawar kasar Bobi Winena tsare a gida, ba tare da samun damar amfani da kafofin sadarwa ba. Kasa da mako guda da tabbatar da Shugaba Yoweri Moseveni a matsayin wanda ya samu nasara a kan 'yan takara tara a zaben shugaban kasar,  kasashen duniya na nuna alamun matsin lamba ga shugaba Moseveni. Ofishin jakadancin Amirka a Kampala ya yi tir da yi wa ofishin babbar jam'iyyar adawa da kuma gidan Wine kawanya, tare da yi wa 'yan fafutuka da 'yan jaridu barazana.

Karin Bayani: Zabe cikin matsalar tattalin arziki

A farkon wanna mako ne gwamnatin Yuganda da zargi jakadan Amirka a kasar Natalie E Brown da yunkurin yi wa zaben da aka gudanar zagon kasa, bayan da ya yi kokarin ziyartar Bobi Wine a gidansa.

Uganda Wahl Robert Kyagulanyi Bobi Wine
Madugun adawar Yuganda Robert Kyagulanyi da aka fi sani da Bobi WineHoto: Sumy Sadruni/AFP/Getty Images

A nata bangaren kasar Birtaniya, ta nuna sassauci sukar gwamnatin ta Yuganda, inda ta yaba da yadda aka gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali ta kuma yi na'am da nasarar Shugaba Mosevenin a Yuganda. Sai dai duk da haka Moseveni ba zai tsira da shan suka ba a wannan sabon wa'adin mulkin da ya kama a cewar Alex Vine na Cibiyar Raya Dimukuradiyya ta Chatam House da ke Birtaniyan.

Karin Bayani: Bobi Wine ya zame wa Yuganda ala-kakai

Zaben na Yugandan dai na ci gaba da samun sakonnin barka da aka saba bisa al'ada, musamman daga kasashen makwabta kamar Tanzaniya da Kenya. Sai dai babban jami'an diplomasiyyar kungiyar Tarayyar Turai  Josep Borrell, ya yi tir da zaben kwana guda da kafin kada kuri'a. Mutane 10 kacal dai gwamnatin Yugandan dai ta bai wa damar zuwa sanya ido kan zaben cikin mutane 1,900 da suka nemi izini daga kungiyoyin farar hula. Yanzu haka dai wani lauyan Najeriya Femi Falana ya shigar da karar gwamnatin Yuganda a madadin Bobi Wine kan tsare shi a gida da jami'an tsaro suka yi tun bayan kammala zabe.