Bobi wine: Sojoji sun yi wa gidana kawanya | Siyasa | DW | 18.01.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bobi wine: Sojoji sun yi wa gidana kawanya

Jagoran adawa a Yuganda Bobi Wine yace sojoji na ci gaba da killace gidansa da shalkwatar jam'iyyarsa ta National Unity Platform a daidai lokacin da yake shirin kalubalantar sakamakon zaben a kotu.

A ranar hudu ga wannan wata na Janairu da muke ciki ne dai, aka gudanar da babban zaben na kasar Yuganda, wanda kuma ya bai wa shugaba mai ci Yoweri Museveni nasara. Sai dai tuni jam'iyyar National Unity Platform ta madugun adawa da ya kasance tsohon mawaki da ya zama dan majalisa Robert Kyagulany da aka fi sani da Bobi Wine ta bayyana cewa za ta kalubalanci sakamakon zaben da ta bayyana da cewa an tafka magudi a gaban kuliya. Tun dai gabaniin zaben ne Wine da magoya bayansa ke fuskantar babban kalubale daga mahukuntan Yuganda. A wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Reuters, Wine ya bayyana cewa sojoji sun mamaye shalkwatar jam'iyyarsu, abin da ya ce ya zama tamkar ana bibiyar duk wani dan jam'iyyar su.

Uganda Wahl Robert Kyagulanyi Bobi Wine

Jagoran adawa a Yuganda Robert Kyagulanyi, Bobi Wine

 "Na samu labarin sojoji sun mamaye ofishin jam'iyyarmu baki daya, kuma har yanzu ban ji daga bakin shugabannin jam'iyyar ba, sai dai ina da tabbacin dukkansu ana bibiyarsu. Kowa ya tsere. Koda matata ta yi kokarin fita domin samo mana abinci, sojoji sun hana ta, kuma sun yi ta jan ta suna taba mata jiki ta hanyar cin zarafinta."

A ta bakin kakakin rundunar 'yan sandan kasar Patrick Onyango sun mamaye shalkwatar jam'iyyar ta National Unity Platform (NUP) ne saboda dalilai na tsaro, sai dai bai yi wani karin haske kan ko sojoji sun shiga harabar ofishin jam'iyyar ba. Rahotanni dai sun nunar da cewa har kawo yanzu Bobi Wine na karkashin daurin talala. Da yake jawabi ga manema labarai lauyan Wine Benjamine Katana ya nunar da cewa:

Uganda Festnahme Robert Kyagulanyi aka Bobi Wine

Jami'an tsaron Yuganda na harba hayaki mai sa hawaye

"A matsayina na lauyansa, ba za mu iya zuba idanu muna ganin ana take masa hakkinsa ba. Muna shaidar da cewa zamu dauki matakin shari'a, da suka hadar da zuwa kotu domin ganin an kawo karshen tsare shi da shi da matarsa da ake yi ba bisa ka'ida ba. Muna bukatar gwamnati ta girmama hakkin Kyagulanyi. Ai fafatawa a zabe ba laifi ba ne."

Ita ma a nata bangaren Ann Reismann shugabar sashen kwararru ta gidauniyar Conrad Adeneur ta Jamus da kuma ke bin batun zaben Yugandan sau da kafa, ta ce sun san Bobi Wine na karkashin daurin talala ta na mai cewa:

"Bayanan da mahkunta ke bayar wa shi ne wai sun tsare shi ne domin tsaron lafiyarsa, sai dai babu wanda aka bari ya gana da shi, an hana lauyoyinsa da 'yan jarida da mambobin jam'iyyarsa zuwa wajensa. Al'ummar kasar na saka ayar tambaya dangane da wannan bayani na mahukunta, musamman idan aka yi, la'akari da yadda yakin neman zaben ya kasance."
 

A jawabin da ya yi bayan da aka bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben Museveni cewa ya yi.

Uganda Wahl 2021 | Yoweri Museveni, Präsident

Shugaban Yuganda Yoweri Museveni

"Ina mika godiyata ga al'ummar Yuganda kuma ina taya ku murnar fitar dango da kuka yi domin zabar dan takara da kuma jam'iyyar da kuke so. Ina ganin wannan ya kasance zabe mafi sahihanci da aka gudanar a  Yuganda tun shekara ta 1962. Wannan ya faru da taimakon iya tantance wadanda suka kada kuri'a ta hanyar amfani da na'urar computer, domin gane cewa babu wani bayan Museveni."

Wannan sakamakon zabe dai ya kara ta'azzara rashin jituwar da ake fama da shi a tsakanin al'ummar Yuganda, a cewar Ann Reismann shugabar sashen kwararru ta gidauniyar Conrad Adeneur ta Jamus da kuma ke bin batun zaben Yugandan sau da kafa, ya kamata kungiyoyin fararen hula su mike tsaye wajen yin kira ga mutane dangane da muhimmancin zaman lafiya, kamar yadda suka yi ta yi gabanin zaben ba tare da la'akari da banbancin jam'iyya ko ra'ayin siyasa ba.

Tun dai a shekara ta 1986 ne Museveni mai shekaru 76 a duniya yake mulki a Yuganda, kuma jagoran adawar Bobi Wine ya sha sukar salon mulkin Moseveni cikin wakokinsa da ya yi a baya, inda yake zargin gwamnatin da cin hanci da nuna son kai, zargin da Museveni ya musanta. Kafafen sada zumunta na zamani, sun taka muhimmiyar rawa wajen hada kan magoya bayan jagoran adawa Bobi Wine kana toshe su a ranar zaben ya kara sanya rashin tabbas dangane da sahihancin zaben. Kawo yanzu dai kafar Internet ta fara dawo wa a Yugandan, kwanaki biyar bayan kammala zaben. 

Sauti da bidiyo akan labarin