1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Ukraine na barazana ga Rasha

July 30, 2022

Kasashen Rasha da Ukraine na zargin juna a kan harin da aka kai kan wani gidan yari a gabashin Ukraine inda aka samu asarar rayuka da jikkatar wasu fursusnoni da dama.

https://p.dw.com/p/4Ett6
Ukraine Kiew | Wolodymyr Selenskyj, Präsident
Hoto: Ukrainian Presidential Press Off/Planet Pix via Zuma/picture alliance

Bayan harin ne dai Shugaba Volodymyr Zelenskyy na Ukraine ya zargi Rasha kai tsaye da aikata kisan kiyashi a kan fursunoni yaki na Ukraine.

Cikin sakonsa na daren ranar Juma'a, Shugaba Zelenskyy ya ce lallai martani zai biyo bayan wannan hari da ta dora alhaki kan Rasha.

Fursunoni 53 ne dai aka tabbatar da mutuwarsu a harin, wadanda kuma a baya su ne suka yi aikin tsaro a yankin Mariopol kafin Rasha ta karbe iko da yankin cikin makonnin da suka gabata.

Kungiyar ba da agaji ta duniya Red Cross, na neman damar shiga yankin domin yi wa mutum 75 da ke fama da raunuka magani.