Shugaban Turkiyya ya yi barazanar daukar fansa kan gwamnatin Siriya | Labarai | DW | 12.02.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Turkiyya ya yi barazanar daukar fansa kan gwamnatin Siriya

Kasar Turkiyya za ta kai hari kan dakarun gwamnatin Siriya a ko-ina cikin Siriya matukar an sake ji wa wani sojin Turkiyyar rauni.

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a wannan Laraba ya ce kasarsa za ta kai hari kan dakarun gwamnatin kasar Siriya a ko-ina cikin Siriyar matukar an sake ji wa wani sojin Turkiyyar rauni.

Erdogan ya fada wa wani taron jam'iyyarsa a birnin Ankara cewa Turkiyya ta kuduri aniyar mayar da hannun agogo baya na nasarorin da sojojin Siriya suka samu a lardin Idlib da ke arewa maso yammacin kasar.

Ya ce: "Daga yau matukar an yi wa sojojinmu rauni kuma komin kankantarsa, za mu kai farmaki kan sojojin gwamnati a ciki da wajen iyakokin lardin Idlib, ba tare da la'akari da yarjejeniyar Sochi ba."

Karkashin yarjejeniyar Sochi da aka cimma tsakanin Rasha da Turkiyya a shekarar 2018, Turkiyya ta kafa sansanonin sanya ido guda 12 a Idlib, inda kuma take mara wa wasu kungiyoyin 'yan tawaye baya.

Akalla sojojin Turkyya 13 aka kashe a wani harin bindigogin atileri na Siriya a wannan wata.