1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Mai ke tsakanin gwamnati da NLC?

August 29, 2024

A wani abun da ke zaman kokarin kauce wa fito-na-fito tsakanin gwamnatin Najeriya da kungiyar kodagon kasar NLC, wani goron gayya na jami'an 'yan sanda ga jagoran kodagon ya kare 'yan kallo a lafiya 'yan wasan ma a haka.

https://p.dw.com/p/4k3kx
Najeriya | Abuja | NLC | Zanga-Zanga
Kungiyar kodogon Najeriyar dai, ta jima tana takun saka da gwamnatocin kasarHoto: Marcus Ayo/AP/picture alliance

Tuni dai sun yi gangami da ma daurin damara, kuma sun ce sun shirya hawa tituna da ma rufe daukacin ofisoshin aiki a cikin Tarayyar Najeriyar. To sai dai kuma 'ya'yan kungiyar ta kodagon kasar sun kare a salama, bayan da shugabansu Joe Ajearo ya mika kansa ga rundunar 'yan sanda ta kasar. Tun da farkon fari dai rundunar 'yan sandan na zargin shugaban NLC da samar da kudi ga ayyuka na ta'adda, ko bayan yin zagon kasa ga kasar. Zargin kuma da ke iya kai wa ya zuwa dauri irin na baba ta gani, a karkashin dokokin Tarayyar Najeriyar. To sai dai kuma akasi na tunani na masu kodagon da ma ragowar jama'ar cikin gari, 'yan sandan sun kare da sakin Ajearo da ya samu rakiyar manyan lauyoyi da ma abokan taku na kungiya ta kodagon. Ita kanta ganawar da sakamakon da ta haifar, na jawo damuwa bisa bambancin da ke tsakanin matsayin 'yan sandan a tun da farkon fari da kuma sauyin da ya biyo matsa lambar jama'ar cikin gari.

Najeriya | Abuja | NLC | Zanga-Zanga
Ba yanzu dai aka saba samun takun saka tsakanin NLC da gwamnatin Najeriya baHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

Isa Sanusi dai na zaman shugaba na kungiyar Amnesty International da ke kokari na kare hakkin dan Adam, kuma ya ce matakin 'yan sandan na da babban sakon aiken tsoro a zuciya ta da dama cikin kasar. Kokarin bin doka ko kuma neman tsoratar da masu kodagon dai, an dauki lokaci ana zargin masu kodagon da karkata zuwa ga adawa. NLC dai, ita ce ta kai ga haihuwar labour party da sannu a hankali ke neman zama kadangaren bakin tulu a zuciyar 'yan mulki. To sai dai kuma matakin 'yan sandan a tunanin Yunusa Tanko da ke zaman kakakin dan takarar shugaban kasar a Labour Party na kasar, ba ya shirin tsorata masu adawar da ke da babban buri na kwace goruba wajen 'yan gado. Abun jira a gani dai na zaman tasirin gayyatar 'yan sandan, ga kungiyar ta kodagon da ke neman fara aiwatar da mafi karancin albashi nan take da kuma gwamnatin da ke fadin ana bukatar kudi.