Shugaban Nijar ya yi waiwaye kan salonsa na mulki | Siyasa | DW | 07.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shugaban Nijar ya yi waiwaye kan salonsa na mulki

Shugaba Mahamadou Issousfou na Nijar ya yi bikin cika shekaru hudu a kan madafun iko. Sai dai da dama daga cikin 'yan kasar sun yi korafe-korafe game da halin kunci rayuwa da suka samu kansu a ciki.

Jam'iyyar PNDS-Tarayya da ke mulki a Nijar da kuma sauran wadanda take kawance da su gudanar da shagulgula don tunawa da kewayowar ranar da Mahamadou Issoufou ya dare kan kujerar mulki shekaru hudun da suka gabata. Su ambato rawar da shugaban ya taka wajen ciyar da Jamhuriyar Nijar gaba, inda suka ce ya kawo sauyi a fannin tattalin arziki musamman wajen inganta harkar hako ma'adanun karkashin kasa. Sannan kuma ya yi yaki da cin hanci da karbar rashawa. Bugu da kari kuma ya maida hankali sosai kan batun tsaro musamman ma yaki da Boko Haram da ta fara kai hare-hare a wani yaki na Nijar.

Rarrabuwar kawuna kan aikin Issoufou

Wasu 'yan Jamhuriyar Nijar sun nuna damuwa kan salon shugabancin shugaba Mahamadou Issoufou inda suka kalubalanceshi kan irin alkawuran da ya yi ba tare da cikawa ba, musamman ma shirin nan na "Dan Nijar ya ci da dan Nijar". Sai dai kuma wasu 'yan kasar ta Nijar suka ce harkokin noma da kiwo sun inganta a cikin shekaru hudu na mukin Mahamadou Issoufou.

Shugaban kasar ta Nijar Mahamadou Issoufou bai mata ganawa da manema labarai ba domin bayyana musu aiyukan da ya gudanar ba. Wannan dai shi ne karon karshe da zai yi irin wannan biki, kasancewa a shekaru ta 2016 ne za a gudanar da zaben shugaban kasa a Jamhuriyar ta Nijar.

Sauti da bidiyo akan labarin