1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Faransa na ziyarar Afirka

July 18, 2014

Ana samun ra'ayoyi masanbanta kan ziyarar Shugaban Faransa Francois Hollande zuwa wasu kasashen Afirka

https://p.dw.com/p/1CfDu
Hoto: picture-alliance/dpa

Tattalin arziki da tsaro su ne mahimman abubuwan da ran gadin da Shugaban Faransa Francois Holland a wasu kasashen yammacin Afirka zai kunsa, sai dai a wasu yankunan, ziyarar tana shan kakkausar suka domin zai yada zango a kasar Cadi wajen Shugaba Idriss Deby wanda wasu suke wa kallon shugaban kama karya.

Bayan da ya je Côte d'Ivoire da Jamhuriyar Nijar, Shugaba Francois Holland zai isa birnin N'Djamena na kasar Cadi da yammacin Jumma'a domin ganawa da takwaransa Idriss Deby wanda ya hau kujerar ikon kasar sakamakon juyin mulki a shekarar 1990, wanda kuma ake kallon ba ya aiwatar da mulki bisa shika-shikan demokaradiyya.

Tschad Pressekonferenz von Präsident Deby
Hoto: AP

Lokacin da ya marawa Faransa da Majalisar Dinkin Duniya baya da dakarunsa a yake yakin wadanda suka addabi kasashen yankin kamar Mali an rika masa kallon cewa idan dai ana so a yi yaki ba zai taba yiwuwa ba tare da shi ba, amma kuma a cikin kasarsa yana shan suka, inda masu sharhi ke ganin cewa ya sami karbuwa wajen jama'a ne kawai saboda dakarun da ya ke turawa wajen wanzar da zaman lafiya.

Dangantakar Faransa da Chadi ba yau ta fara ba, tsohuwar uwargijiyar na ta, ta dade tana kula da wannan dangantakar bisa wasu dalilai na san ranta. A shekarar 1990 Deby ya hambarar da magabacinsa Hissene Habre. A shekara ta 2008 kuma ya fara neman tallafi bayan da wasu 'yan tawaye suka yi kokarin tuntsurar da shi daga kujerar mulki.

Tschad Militärparade
Hoto: picture-alliance/dpa

Haka nan kuma ga Faransar makwabciyar Cadin, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya tana da mahimmancin gaske, ba dan tattalin arziki kadai ba, ko dan samun gindin zama a yankin. A biranen N'Djamena da kuma Abeche da ke yankin kudancin kasar, Faransa tana da sansanoni biyu na soji, kuma N'Djamena tana da mahimmanci saboda nan ne za a rika ajiye dakarun yaki da ta'addancin da Faransa ta shawarci a girka.

Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Suleiman Babayo