1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Chadi Mahamat ya ziyarci Bazoum

Gazali Abdou Tasawa
May 10, 2021

Shugaban gwamnatin soji ta rikon kwarya a Chadi Janar Mahamat Deby ya kai ziyara Nijar inda ya gana da shugaba Mohamed Bazoum a fadarsa a birnin Niamey.

https://p.dw.com/p/3tCsE
Niger | Besuch tschadischer Präsident Mahamat Idriss Deby
Hoto: Präsidentschaftsbüro Niger

Shugaban kasar ta Chadi da tawagarsa sun sami kyakkyawan tarbe daga firamnistan kasar Nijar Mahamadou Ouhoumoudou wanda ya tarbo tawagar daga filin jirgi zuwa fadar shugaban kasa. Shugabannin kasashen biyu sun yi ganawar sirri akan batun diflomasiyya da yaki da ta'addanci. 

Ya ce mun zo a nan ne domin jaddada amintakanmu da Nijar da kuma isar da godiyarmu ga Shugaba Mohamed Bazoum kan irin goyon bayan da yake kawo mana tun bayan rasuwar Marechall Idriss Deby. Muna da sojoji sama da 1000 da ke girke a yankin Tera a karkashin rundunar G5 Sahel don haka muka zo mu ziyarce su mu isar masu da ta’aziyyyar rasuwar shugaba Idriss Deby mu kuma basu kwarin gwiwa a aikin da suke yi.   

Wannan dai ita ce ziyar ta farko da sabon shugaban kasar Chadin Janar Mahamat Idriss Deby ya kai a wata kasa tun bayan hawansa mulki. Malam Siraji Issa shugaban kungiyar Mojen yace ziyarar na cike da ma’ana ta la’akari da cewa ita ce ta farko da sabon  shugaban na Chadin ya kai wata kasa tun bayan hawansa mulki.

Shi ma Malam Abdourahmane Alkassoum mai sharhi kan harkokin tsaro a Nijar na ganin wannan ziyara ta shugaba Mahamat Idriss Deby da ke zama ta farko a jerin rangadin da yake shirin ka iwa a kasashen G5 Sahel   da cewa ziyara ce da za ta karfafa matakan soja a fagen yaki da ta’addanci a yankin sahel baki daya

Abun jira a gani shi ne tasirin da ziyarar ta shugaba Deby a Nijar da sauran kasashen G5 Sahel za ta yi wajen kara kaimi a yaki da ta’addanci a yankin .