1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Yan tawaye a Chadi sun shirya sasantawa da gwamnati

April 25, 2021

'Yan tawaye a Chadi  da suka addabi arewacin kasar a cikin makonni biyun da suka gabata kuma sojojin kasar suka ce sun kashe tsohon shugaban kasar Idriss Deby, sun ce a shirye suke su tsagaita wuta.

https://p.dw.com/p/3sXPc
Tschad I Militärische Operation gegen Rebellen in Ziguey
Hoto: Abdoulaye Adoum Mahamat/AA/picture alliance

A cikin hirarsa da kamfanin dillancin labarai na Faransa na AFP, shugaban 'Yan Tawayen da ake wa lakabi da FACT Mahamat Mahadi Ali ya tabbatar da aniyarsu ta tsagaita wuta da cimma matsaya da gwamnati. 

Sai dai Mahadi Ali ya yi gargadin cewa idan har ana son ganin hakan dole sai bangaren sojojin Chadi shi ma ya tsagaita wuta, yana mai cewa ba za su zura ido su ga dakarun gwamnati na kashe su ba tare da sun rama ba.

Da yake mayar da martani a kan wannan batu, mai magana da yawun majalisar soji da ke mulkin Chadi ya ce sojoji na na yi wa mutanen na kungiyar FACT lugudan wuta ne saboda 'yan tawaye ne kuma abin da hukuma za ta iya yi musu ke nan.