1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

SHUGABA RAU YA YI JAWABIN BAN KWANA A BIRNIN BERLIN.

YAHAYA AHMEDMay 12, 2004

Shugaban kasar tarayyar Jamus, Johannes Rau, ya yi jawabinsa na ban kwana a birnin Berlin. Shugaban, wanda wa’adin aikinsa zai cika a ran 30 ga watan Yuni mai zuwa, ya takalo batutuwan da a cikin shekarun bayan nan, aka yi ta korafi a kansu ne a nan Jamus, kamar dai batun kaura zuwa nan Jamus, da salon nan na hadayyar tattalin arzikin duniya, ko kuma „Globalisation“ a turance, da kuma irin rawar da Jamus ke takawa a fagen siyasar duniya, a halin yanzu.

https://p.dw.com/p/Bvjf
Shugaban Tarayyar Jamus mai barin gado, Johannes RAU.
Shugaban Tarayyar Jamus mai barin gado, Johannes RAU.Hoto: AP

A cikin muhimmin jawabinsa na karshe kuma na ban kwana, kafin cikar wa’adin aikinsa, a ran 30 ga watan Yuni mai zuwa, shugaban kasar Tarayyar Jamus, Johannes Rau, ya yi kira ga al’umman kasarsa da su karfafa wa juna gwiwa wajen huskantar kalubalen da halin rayuwar yau da kullum ke dauke da shi, su kuma yi imani da kasarsu. Shugaban ya ci gaba da cewa, duk al’ummomin da ba su da imani da kasarsu, to ba za su iya cim ma nasara wajen inganta makomansu ba. A ganin shugaban dai, al’amura ba su tabarbare a nan kasar kamar yadda jama’a ke ta kururuwa ba. Ya dai zargi `yan siyasar kasar ne da jagorancin wannan salon, da kuma cusa wa jama’a ra’ayoyin miyagun fata a kawunansu. A cewarsa dai:-

"Ban san wata kasa a doron kasa, inda masu rike da madafan iko ke da sha’awar yi wa kasarsu babatu da mugunyar fata, kamar a nan Jamus ba."

Ashe ko ba abin mamaki ba ne, inji shugaban, idan jama’ar kasa suka dinga nuna rashin imani ga masu rike da ragamar mulki. Akwai dai misalai da dama na aika-aikar da masu mukami suka yi, wadanda kuma ke sanya jama’a nuna rashin imani gare su:-

"Dukkanmu dai, mun ga yadda wasu masu mukamai a hukuma ko kuma a fannin tattalin arziki, suka yi ta azurta kansu kamar yadda suka ga dama, ba tare da nuna wata damuwa ba. Sanin abin da ya kamata, ko kuma ya dace, ya zamo wani bakon salo ne gare su. Son kai, da bin son zuci da ake ta kara samu a bainar masu rike da madafan iko ya dusashe kwarjinin da kafofinmu ke da su, saboda shugabannin wadannan kafofin ba sa nuna wata alama kuma ta da’a wajen gudanad da ayyukansu."

A fagen siyasa dai, shugaba Rau ya gargadi da masu jan ragamar mulki, da ka da su yanke shawarwarin da za su janyo fa’ida kawai ga manyan cibiyoyin kasuwanci da na tattalin arziki. Kamata ya yi, inji shugaban, ikon yanke muhimman shawarawarin da za su shafi makomar kasa baki daya, ya koma a Majalisa, amma ba ya saura hannun kwamitocin da ba su da sha’awar kome sai ta ganin sun kare maslahar kamfanonin jari hujja ba. Shugaban ya karfafa cewa, yadda ababa ke wakana yanzu a fagen siyasar dai, bai dace ba. Ya kara da cewa:-

"Rashin sanin abin da ya kamata ne, idan gwamnati ta yi watsi da wata shawara, saboda kawai daga bangaren adawa ta fito, duk da cewa, wannan shawarar tana da ma’ana da fa’ida ga duk kasa baki daya. Kazalika kuma, abin ban takaici ne, ganin yadda `yan adawan ma ke yi wa wasu kyawawan shirye-shirye babakere, saboda daga gwamnati suke, duk da sanin cewa, su ma wadannan matakan za su dauka, idan su ke kan mulki."

Ko wane dan Adam dai na yi wa kansa fatar alheri, inji shugaba Rau. Ko wace kasa ma na bukatar irin wannan fatar idan tana son ta ci gaba. Sabili da haka ne kuwa, shugaban ya yi kira ga duk mazauna nan kasar da su ba da tasu gudummuwa wajen ganin cewa, Jamus ta fita daga cikin matsalolin da take huskanta. Furucin da shugaba Rau ya yi, a karshen jawabinsa na ban kwana ga Jamusawa da kuma duk mazauna nan Jamus, shi ne:-

"Wajibi ne ga ko wane daya daga cikinmu, ya ba da tasa gudummuwa, wajen ganin cewa, a ko wace rana, mun sami ingancin halin rayuwa da kuma nuna zumunci a nan kasar tamu."