1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Shugaba Putin na ziyarar karfafa danganta a China

Binta Aliyu Zurmi
May 16, 2024

Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin na ziyara a kasar China. Ziyarar da ke da nufin kara kula dangantaka a tsakanin kasashen biyu na zama irinta ta farko da Putin ke yi a sabon wa'adin mulki da ya kama a kasarsa.

https://p.dw.com/p/4fuWV
Wladimir Putin und Xi Jingping
Hoto: Mikhail Tereshchenko/Sputnik/AP/picture alliance

Ziyarar Shugaba Vladmir Putin ta kwanaki biyu a China za ta mayar da hankali a kan wasu batutuwa da suka hada da batun rikicin kasarsa da Ukraine da ma wadanda suka shafi kasashen Asia da kuma ta batun kasuwanci a tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Xi Jinping na kasar China ya sha alwashin farfado da dangantakar aiki kafada-da-kafada da kasar Rasha. 

Shugaban ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar da Shugaba Vladmir Putin na Rasha ke yi a kasar.

A yayin ganawar farko da suka yi a babban zauren taro na Great Hall a Beijing, China ta sake jaddada cewar za ta ci gaba da zama kawa ta amana ga Rasha.

Wannan ziyara ta Putin a China da ke zuwa bayan ya sake darewa madafun iko a karo na biyar na aikewa da sako ga kasashen duniya kan irin shakuwar da ke tsakanin shugabannin biyu, da kasashen yamma ke nuna damuwa a kai.