Shugaba Lukashenko na ziyara aiki a Zimbabwe | Labarai | DW | 30.01.2023
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Lukashenko na ziyara aiki a Zimbabwe

Shugaba Alexander Lukashenko na kasar Belarus ya isa kasar Zimbabwe inda ya samu tarba ta musanman daga Shugaba Emmerson Mnangagwa da mukarraban gwamnatinsa.

Lukashenko da Mnangagwa

Lukashenko da Mnangagwa

Shugaba Alexander Lukashenko na Belarus ya samu tarba ta musanman daga dubban 'yan kasar Zimbabwe da suka yi cincirindo a filin jirgin saman Robert Mugabe da ke babban birnin kasar. Masu sharhi na ganin, ziyara ce ta dabbaka dangantakar diflomasiyya ganin yadda kasashen biyu ke fama da takunkuman da kasashen yamma suka kakkaba musu kan zargin take hakkin dan adam da kuma yadda ita Belarus ta kasance babban aminiyar Rasha da ba sa jituwa da kasashen Turai. A shekarar 2019 ne Shugaba Emmerson Mnangagwa ya kai wa Lukashenko ziyara a birnin Minsk.