Shugaba Jonathan ya karbi takardan takara | Siyasa | DW | 30.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shugaba Jonathan ya karbi takardan takara

A karon farko jam'iyyar PDP ta tsaida dan takara daya tilo, inda jam'iyar ta ce takardan dan takara daya suke da ita, don haka dan takaransu shi ne shugaba kasa mai ci,

A wani abun da ya tabbatar da karshen taci ba taci ba a bisa takarar shugaban tarrayar Najeriya Goodluck Ebele Jonathan, da ranar yau shugaban kasar ya yi ta-maza wajen sayen takardan tsayawa takarar a karkashin jam'iyyar PDP a zaben dake tafe.

A wani bikin da ya samu halartar jiga-jigan yayan jam'iyyar dai, shugaban ya kira takarar tasa a matsayin alamu na gamsuwar al'ummar kasar, bisa salon mulkin da yake tafiyarwa a kasar. An dai hanawa wasu mutanen biyu samun takardar takaran jam'iyyar ta PDP. Inda aka bar shugaba Jonathan shi kadai ya tsaya, wannan kuwa shi ne karo na farko da jam'iyyar PDP ta yi haka tun lokacin da aka kafa ta a shekara ta 1999.

To sai dai kuma shugaban da bashi aboki na karawa a cikin jam'iyyar da ta fidda salon hanawa kowa takara kan mukamin na shugaban kasa, yana shirin tunkarar yan kasar ta Najeriya, adai dai lokacin da rashin tsaro da talaucin wadanda suka rinjayi gwamnatinsa na lokaci mai tsawo.

Sauti da bidiyo akan labarin